Jawabi Shugaban PDP na kasa, Alh Labiru Tanimu Turaki, SAN ga manema labarai game da hukuncin Kotun Tarayya danke Ibadan
Mun samu labarin hukuncin Kotun Tarayya da ke zama a Ibadan, wanda aka yanke a safiyar yau. Hukuncin ya ƙi bayar da umarnin tilastawa (mandamus) da muka nema, bisa dalilin cewa bayar da irin wannan umarni, a fahimtar kotun, zai zama kamar kotun na zama kotun ɗaukaka ƙara ne a kan hukuncin wata kotu mai matsayi iri ɗaya da ita.
Don fayyacewa, mun kai ƙara kotu ne domin neman umarnin tilastawa (mandamus) da zai tilasta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta amince da Taron Jam’iyyar PDP na Ibadan tare da sauƙaƙa mu’amalar hukuma da jam’iyyar.
A yayin shari’ar, wasu tsoffin mambobin jam’iyyarmu, waɗanda aka kora a baya, sun nemi a shigar da su cikin shari’ar, kuma kotu ta amince da hakan. Sun shigar da ƙorafe-ƙorafe suna roƙon kotu da ta ƙi amincewa da bukatunmu, ba tare da ƙarin bayani ba.
Sai dai, cikin girmamawa, kotun ta ɗauki matakin (suo motu) da kanta) ta bayar da wasu umarni da ba a nema ba kuma babu wani ɓangare da ta tattauna da su. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, hukuncin yana cikin saɓani kai tsaye da wasu umarni da hukuncin kotuna masu matsayi iri ɗaya da ke nan daram.
Sakamakon haka, mun riga mun shigar da Sanarwar Ɗaukaka Ƙara (Notice of Appeal) tare da Buƙatar Dakatar da Aiwatar da Hukunci (Motion for Stay of Execution), kuma mun kuduri aniyar bin wannan lamari da ƙwazo har zuwa ƙarshe bisa tanadin doka.
Domin kauce wa ruɗani, wannan hukunci ɗaya ne kacal daga cikin hukunce- hukunce da dama da Kotun Tarayya ta yanke a kan wannan batu, kuma manyan batutuwan da suka taso daga gare su sun riga sun isa gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara. A wannan fahimta, wannan hukunci na musamman, a fannin shari’a, hukunci ne na wucin gadi, yana jiran cikakken hukunci daga kotunan ɗaukaka ƙara.
Ina so in tabbatar wa dukkan mambobin jam’iyyarmu mai girma cewa, duk da wannan hukunci, Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) da Taron Ibadan ya samar yana nan daram dam bisa doka, kuma yana ci gaba da jajircewa wajen sake farfaɗo da Jam’iyyar PDP.
Saboda haka, ina kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar a faɗin ƙasar nan da su zauna lafiya, su kasance masu natsuwa da jajircewa. Babu ko kaɗan dalilin firgici. Motsin Sake Haihuwa (REBIRTH) yana tafiya bisa tsari.
Wannan hukunci ba komai ba ne illa wucewa ta ɗaya daga cikin lanƙwasa hanyoyin shari’a a tafiyarmu. Manufar ƙarshe tana nan a sarari, kuma kamar yadda tarihi ya nuna a kai a kai, abin da ya fi muhimmanci shi ne sakamakon ƙarshe.
.














