Batun sakin ‘yan ta’adda a Jihar Katsina

198

Daga Maiwada Dammallam A baya bayan nan babu abin da ya dauki hankalin al’umma kamar labari da ya fito a jaridar Sahara Reporters mai dauke da cewa gwamnatin Jihar Katsina ta shiga yarjejeniyar sakin wasu ‘yan ta’adda kimanin 42 wadanda ke tsare a hannun hukumomi don gurfana gaban kuliya.

Mutane da dama sun bugo mani waya, wasu kuma sun zo takanas sun same ni, suna so su ji ba’asin maganar. Da yawan su sun nuna bacin rai kan wannan mataki da suka ji gwamnati za ta dauka. Na yi masu bayanin kamar yadda zan kara yin bayani a nan.
Da farko dai na yi kokarin su fahimta cewa maganar tsaro magana ce mai bukatar sirri; ba magana ba ce wadda ta dace da dandalin yanar gizo, ko wadda za a yi da gama – garin mutane. Magana ce wadda ke bukatar sirri da kuma bukatar abu biyu: Na farko a fahimce ta sosai kafin a yanke hukuncin an yi daidai ko akasin haka. Na biyu kuma ya zamanto an samu mafi sahihancin bayani kan lamarin da ake tattaunawa.
Ko a gwamnatance, maganar tsaro ba kowa da kowa ke sanin abin da ake ciki ba, ba kuma kowa ake sawa ba. Wannan kuma ba a Katsina kawai wannan tsarin ya ke ba. Duk duniya, ko ina haka abin yake. Da yawa mutum zai ga maganar tsaro kamar ta yi gabas, sai ya bi ta; ya yi gudu ya gaji sannan ya gane ashe yamma maganar ta yi.
Gwamanti na da talala kan maganar tsaro. Da yawa mutane sai suga kamar wani munafunci ko son zuciya ke sa gwamnati ba ta fitowa ta fadi me ta ke ciki kan maganar tsaro. Ba kuma haka ba ne. Da yawa bayanin ba na fitarwa ba ne don yana cikin shirin ta na sirri na samun nasarar abin da ta sanya a gaba. Da yawa abin da mutane suke so su ji daga bakin gwamnati, idan ta fito ta fadi abun to ba ya da sauran amfani akan tsarin ta.
 Akan maganar tsaro gwamnatoci har karya suna iya yi don al’umma su zauna lafiya. Misali, Yau idan gwamnati ba ta da kudin sayen harsashi don ba jami’an tsaro, tana iya karya ta ce ta sawo harshashi na biliyoyin naira don ta ci da buguzum ta tsoratar da abokan fada. To lallai akwai bukatar a fahimta cewa maganar tsaro ta wuce a baje m a jaridu ko a yanar gizo.
Akan wannan dambarwar, abin da ya faru shine:
Kowa yasan shiri da Kananan Hukumomi daban daban suka shiga na sulhu da ‘yan ta’adda don samun zaman lafiya. Duk da cewa gwamnati ta dauki matsayar cewa ba za ta nemi wani dan ta’adda tayi zaman sulhu da su ba,  ba ta rufe Kofar sulhu da duk wani dan ta’adda da ya ga kyautatuwar ya ajiye makami, ya rungumi zaman lafiya ba. Akan haka gwamnati ta saurari bukatun mutane daga kananan hukumomi daban-daban da suka zo neman a ba su damar su yi zaman sulhu da ‘yan ta’addan da suka nemi a yi hakan. Gwamnati ta ba su damar yin hakan tare da tabbacin bayar da goyon baya duk inda hakan ya dace kuma ta duk hanyar da ba ta saba ma doka ba.
Mal Maiwada Danmalam
Hakan ya ba kananan hukumomi daban-daban dama suka assasa zaman sulhu da ‘yan ta’addan da suka addabe su; kuma cikin yardar Allah aka samu nasarorin kawo zaman lafiya a wurare daban-daban ta inda har wurare da ada babu mai iya shiga, yanzu kowa na shiga ya fita cikin aminci da zaman lafiya.
Hakrokin yau da kullum sun dawo a wurare da yawa. Kasuwanni da aka rufe a dalilin rashin tsaro, gonaki da aka bar zuwa duk a dalilin rashin tsaro, yanzu duk an koma ana ta hada-hadar yau da kullum.
A baya, lokacin zaman sulhun, akwai bukatu da bangorin biyu suka gabatar ma juna don tabbatar da zaman lafiyar da aka samu. Ciki akwai bukatar da al’umma suka ba ‘yan ta’adda ta sakin duk wani wanda ke rike a hannusu don amsar kudin fansa. ‘Yan ta’addan kuma suka yarda cewa za su sako duk wanda ke hannunsu tun da yanzu an ce sulhu aka yi kuma zaman lafiya da yarda da juna za’a ci gaba da yi. A nasu bangaren kuma sun bukaci gwamnati ta sako masu wasu mutunen da ke hannun hukumomi suna jiran kuliya. Shugabanni kasa da na kananan hukumomi wadanda suka jagorinci zaman sulhun suka ba ‘yan ta’addan tabbacin cewa ba su da wannan karfin da za su zartas da wannan hukuncin amma za su kai koken gaba don ganin an yi hakan don samun zaman lafiya mai dorewa.
Haka kuma aka yi. Kananan Hhukumomi daban-daban sun zo sun kawo ma gwamnati koken hakan (kamar yadda gwamnati ta bukata don sa ido kan lamarin), sun kuma nuna muhimmancin cika wannan sharadin don samun zaman lafiya mai inganci.
 Gwamnati ta tuntubi masana tsaro na cikin gida da na waje kan dadewar yin hakan, duk kuma ta samu tabbacin cewa abu ne da dama duk inda ake neman yin sulhun irin wannan matsalar yana iya bijirowo kuma da yawa ana bayar da damar hakan don samun zaman lafiya.
Gwamnati ba ta yi kasa a guiwa ba, ta koma neman kididdigar mutanen da ke hannun ‘yan ta’addar ta kuma gano cewa akwai mutane fiye da dubu a hannun ‘yan ta’adda daban-daban wadanda ba’a san halin da suke ciki ba. Daga nan gwamnati ta yarda za ta sa baki a sako mutum 42 na ‘yan ta’addan da ke rike gidan kaso amma sai idan sun fara sakin mutanen da aka tantance cewa suna rike a hannunsu. Haka kuma aka yi. Shugabanni kananan hukumomi tare da iyayen kasa da jami’an tsaro a lokutta daban-daban sun karbi mutane da ‘yan ta’adda suka bayat da karkashin wannan yarjejeniya.
Ta wannan tsarin an kubutar da mutane kamar haka:
Karamar Hukumar Safana mutane 36, Kurfi mutane 42, Faskari mutane 136, Sabuwa mutane 310, Danmusa mutane 60, Malumfashi mutane 36, Bakori mutane 125, Musawa mutane 28, Matazu mutene 33, Dutsinma mutene 62, Jibia mutane 31. Ba duka ba ke nan. Akwai adadin daban da ba samu ba zuwa yanzu.
Gwamnati, tare da iyayen kasa an zauna an auna ribar cika ma ‘yan ta’adda alkawarin da iyayen kasa suka daukar masu na lallashin gwamnati ta duba kyautatuwar sakar masu mutanen da suka roka a saki, an kuma samu gamayyar cewa ribar sakin mutane ta fi rashin ribar yawa. Kan haka aka dauki matakin cika wannan alkawari.
Bidiyo da na hado da wannan k’asidar na mutanen da irin wannan tsarin ya kubutar ne a Karamar Hukumar Malumfashi wadanda tsohon dan ta’adda Mustapha Babaro ya jagoranci kubutar da su, ya kuma kawo ma iyayen kasa, mutene 36 maza, mata da yara wanda akan haka ya roki gwamnati ta sakar mashi mutum 2 kachal.
Abin kula:
Gwamnati ba ta dauki wannan matakin don nuna ko-in-kula da halin da ‘yan ta’adda suka sa jama’a a baya ba. Ta dauki matakin ne domin shi yafi dacewa da yanayin da aka shiga na ta’azzarar matsalar tsaro da kuma neman yadda za’a zaunar da al’umma lafiya, a tsaida zubda jini da asarar rayuka na ba gaira ba dalili.
Masu fashin baki daban-daban suna kallon lamarin daga mahanga daya ce kawai — cewa an kama mai laifi amma an ce an sake shi. Ba su duba mahangar me ke ribar sakin shi din. Misali, a baya-bayan nan akwai ‘yan ta’adda da aka yi sulhu da su, da ke mara ma gwamnati baya wajen yaka tare da dakile hare-hare da wasu ‘yan ta’adda da ba su yadda da tsarin sulhu da ke kokarin kai ma al’umma. Ko kwanan nan an fafata tsakanin Mustapha Babaro da dan ta’aada Audu Doro wanda ya kai hari a Karamar Hukumar Malumfashi. Audu Doro dan ta’adda ne da tun lokacin tsohuwar gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari, bai yarda ya karbi goron gayya na zaman sulhun ba.
Ke nan, akwai hikima idan gwamnati ta amince ta goya ma ‘yan taddan da ake da yakinin cewa sun yarda su zauna lafiya da al’umma ta irin wannan hanyar Akalla dai ya kamata mutane sun yarda cewa idan har gwamnati ta taba kama dan ta’adda, to kau tana iya kara kama shi idan ya saba ma sharuddan sakin shi da tasa aka yi. Ke nan, akwai bukatar al’umma su yi ma gwamnati kyakkyawan zato; su fahimci cewa duk matakin da za ta dauka ba da ido rufe za ta dauka ba; sai da tabbatar da cewa shi ne abin da ta gamsu shi ya fi dacewa da al’umma a yanayin da ake ciki.
Yau idan da gwamnati na da karfin tuwon da za ta iya shiga duk inda ‘yan ta’adda suke, ta yake su ne amma aka ga ta koma kan sasanci har an kai ana musayar fursunoni, to sai a zarge ta da yin sanya. To amma kowa ya san ba haka lamarin ya ke ba. Gwamnatin Jiha ba ta da soja ko dan sanda. Ko jami’an tsaro na jeka-na -yi-ka da ta yi bata da hurumin ba su makamai masu inganci irin wanda ‘yan ta’adda ke amfani da da su don dokar kasa ta haramta haka. Ke nan, akwai bukatar a fahimci irin daurin talalar da kundin tsarin mulki ya yi ma gwamnatocin jihohi a kan maganar tsaro don fahimtar irin halin kaka-ni-kayi da suke ciki. Yin haka ne kawai zai bayar da damar a fahimci kokarin da suke yi a karkashin tsarin da suke jagoranci.
Ina so ya zama kalubale ga duk wanda ya ke jin gwamnati ba ta yi daidai ba kan wannan lamarin da ya yi kokari ya zagaya Kananan Hukumomi da na lissafa a sama, ya ji ta bakin mutanen da suka samu kubutarwa don jin ko su ma ba su gamsu da matakin da gwamnati ta dauka ba. Ina da yakinin ra’ayin zai ci karo da na masu fashin bakin da suke kallon abin daga nesa  ta cikin yanar gizo — wadanda ba su da alaka ta kai-tsaye da matsalar.
Zan rufe da addu’ar Allah SWT ya ba shugabanninmu karfin guiwa da hikimar kawo mana zaman lafiya mai dorewa.
Maiwada Danmalam Daraktan Hakrokin Watsa Labaran Fadar Gwa matin Jihar Katsina
Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here