Kaduna: Shugabar matan SDP ta fice

151

Shugabar Matan SDP a jihar Kaduna Hajiya Zainab Sani, ta bayyana ficewa daga jam’iyyar, a daidai lokacin da jam’iyyu SDP da ADC ke kokarin hadewa dommfuskantar APC a zaben 2027.

Hajiya Zainab Sani, wadda ta fito daga karamar hukumar Giwa, ta shahara wajen karfafa halartar mata a harkokin siyasa da kuma wayar da kan jama’a a fadin jihar.

Ta taka rawar gani wajen kawo nasarorin jam’iyyar APC a lokutan zabuka, kafin ta koma SDP inda ta zama muryar mata mai ƙarfi da kuma amintacciyar abokiyar siyasa ga El-Rufai.

Yayin da ta ke sanar da ficewarta daga jam’iyyar, Hajiya Zainab ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda SDP ta kasa gabatar da manufofi masu mayar da hankali kan talakawa, tana zargin jam’iyyar da zama tamkar mafakar ‘yan siyasar kima maimakon mayar da hankali kan bukatun al’umma.

 “SDP ta kasa nuna cewa jam’iyyar talakawa ce, Mutanenmu na fama da talauci, rashin tsaro, da yunwa. Yawancin jama’ar Kaduna ba su manta da manufofin da suka cutar da su a lokacin gwamnatin baya ba, kuma ba zan kasance cikin wani shiri da zai sake tsarawa wannan tarihi da sabon suna ba.”

Kalamanta  na nuni da yadda wasu jama’a ke ci gaba da jin haushi kan wasu manufofin tsohon gwamnan, ciki har da rushe-rushe na gine-gine, korar ma’aikata, da sabani da ƙungiyoyin ƙwadago da al’umma.

Ficewar Zainab ta zo ne a daidai lokacin da Gwamna Uba Sani ke ƙara tabbatar da mulkinsa mai taimakon jama’a, ta hanyar manufofin raya karkara da ci gaban al’umma   wanda ke samun goyon baya sosai a fadin jihar.

Gwamnatin Uba Sani ta mayar da hankali kan ƙarfafa al’umma, rage talauci, da haɗa kowa da kowa  abin da ke bambanta da tsarin siyasar masu kima da ake cewa ya mamaye SDP a yanzu.

Masana siyasa sun bayyana cewa ficewar Zainab babban rashi ne a fannin siyasa da kuma alama ga bangaren El-Rufai. Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan yana cikin tattaunawa da jam’iyyar ADC domin kafa sabuwar kawancen siyasa kafin zaben 2027.

 “Ficewar Zainab wata gargaɗi ce ga SDP,” in ji wani masani. “Tana da karfin tasiri sosai musamman a tsakanin mata da matasa a karkara. Rashinta a wannan lokaci babbar koma baya ce ga shirin haɗin kai da kuma sahihancin wannan sabon yunƙuri.”

Kodashike ba ta bayyana inda za ta nufa ba, sai dai majiyoyi sun ce ta kammala shirin komawa jam’iyyar APC tare da mata sama da 5000 daga yankunan arewa da tsakiya na jihar  matakin da ya yi daidai da yunƙurin Gwamna Uba Sani na ƙara haɗa kan al’umma a cikin tsarin mulkinsa mai fa’ida ga kowa.

Murabus ɗinta ya ƙara bayyana yadda tsarin siyasa a Kaduna ke canzawa, yayin da shugabannin ƙananan al’umma da masu tasiri ke ta rungumar tsarin mulki na Gwamna Uba Sani wanda ya dogara da tausayi, haɗin kai, da aikata ayyukan da jama’a ke gani da ido   ba kawai gwaje-gwajen siyasar ‘yan kima ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here