Tinubu ya jinjinwa jama’ar Jihar Katsina

581

Dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya yi zama na musamman da shugabannin addinin musulunci na Jihar Katsina a cibgaba da neman goyon jama’a akan zaben shugaban kasa a 2023.

An gudanar da taron ne a babban dakin taro na Gwamnatin Jihar Katsina. Asiwaju Bola Tinubu ya samu rakiyar Gwamnanonin jihohin Katsina, Zamfara, Jigawa, Kebbi, Sanata Abu Ibrahim, Sanata Hadi Sirika, Rt. Hon. Tasiu Zango, Dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC, Dokta Dikko Radda, mataimakin sa, Hon. Faruq Lawal Jobe, Sanata Bello Mandiya, Alh. Nuhu Ribadu, Alh. Ibrahim Masari, da sauran su.

Sheikh Hadi Balarabe a madadin darikar Tijjaniya, yayi ma dan takarar shugaban kasa barka da zuwa Jihar Katsina tare da yi mashi fatan alkhairi da samun nasara a zaben 2023. Ya bada tabbacin cikakken gowon bayan su a madadin darikar Tijjaniya na jihar Katsina da kuma mutanen da suke da alfarmar su.

Wakilin Kungiyar Ahlul sunnah, ya bayyana gamsuwar su kan takarar Ahmed Tinubu da Kashim Shattima a matsayin mutanen da za su kawo ci gaba ga addinin musulunci da kasar Najeriya bakin daya. A karshe ya bayyana cewa sun hada kai domin ba shi gudunmuwa don ganin ya cimma burin shi na zama shugaban Najeriya.

Shi ma dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC, Dr. Dikko Radda, ya bayyana godiyar shi ga malaman jihar Katsina bisa ga irin goyon baya da suka ba Gwamna Aminu Bello Masari wanda a cewar shi, ya kare hakkokin addinin musulunci.

Ya bayyana irin gagarumar gudunmuwa da malaman addini za su bada wajen zaben shugaba nagari, sannan ya yi kira gare su da su kalli dukkanin yan takarar  shugaban kasa su yi masu alkalanci da ayyukan da sukabyi a baya.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana Ahmed Tinubu a matsayin mutum mai kishin Arewa tun a lokacin marigayi Shehu Musa Yaradua. Ya bayyana shi a matsayin mutumen kirki wanda ya yi abun kirki a lokacin da ya ke gwamnan jihar Lagos wanda har yanzu bisa turbar shi jihar ke tafiya. Ya roki alfarmar malaman da su zabi Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya domin kawo ci gaba.

Da yake maida jawabi, Ahmed Bola Tinubu, ya shaida cewa babu abun da zai ce sai godiya ga irin karramawa da karamchi da al’ummar jihar Katsina suka nuna mashi. Yayi godiya ta musamman ga irin gudunmuwar da Gwamna Aminu Bello Masari ya ba shi tun lokacin da zai tsaya takarar shugaban kasa wanda yake alfahari da mutanen jihar Katsina.

Ya gode ma malamai da irin kyawawan fatan alkhairi da suke yi mashi tare da ba su tabbacin cewa zai rike amanar addinin musulunci da al’ummar Najeriya baki daya.

Daga karshe ya mika sakon jaje da alhini ga al’ummar da suka rasa rayukan su ta hanyar yan ta’adda a Bakori da sauran sassan jihar Katsina. Ya kuma bada gudunmuwar Naira miliyan dari (N100,000,000) ga al’ummar da wannan ibtila’i ya fadamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here