EFCC, DSS, ICPC sun yi wa el-Rufa’i kofar raggo

281

Akwai alamun cewa Mal Nasir el- Rufa’i, tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya shiga uku sakamakon tirka- tirkarshi da hukumomi uku, wato Hukumar yaki da rashawa da zambar kudi, EFCC da Hukumar yaki da almundahana, ICPC da kunan hukumar jami’an tsaro ta farin kayan, DSS.

Ya zuwa yanzu el- Rufa’is yana kwana na uku a hannun EFCC ba tare da samun beli ba, kuma yau, Lataba aka shirya zai gurfana gaban ICPC domin amsa wasu tuhume – tuhume da ta ke yi masa, yayin da Hukumar DSS ta kai shi kara a wata kotu bisa zargin ya yi amfani da wasu dabarun satar maganganun Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara akan harkokin tsaro, Mal Nuhu Ribadu.

Bayanai na nuna cewa EFCC ta amince da bayar da belinsa amma bisa sharadin sai wani babban sakatare da ma’aikaci mai mukamin darakta a wasu ma’aikatu sun tsaya masa.

Wasu rahotanni suna bayyana cewa a lokacin da wani babban sakatare ya he EFCC domin ya tsayawa el-Rufa’i game da sharuddan belinsa, sai ya fasa.

EFCC tana tuhumar el-Rufa’I da almundahana da almubazzaracin naira biliyan 433 a lokacin da yana gwamnan Jihar Kaduna, wato tsakanin 2015 da 2023.

Rahotanni suna cewa lauyoyin el-Rufa’i sun rubutawa Hukumar ICPC da tA shirya gurza shi yau Lataba cewa el-Ruda’i ba zai Iya ansa gayyatarsu a yau ba saboda yana tsare a hannun EFCC. Wannan na nuna cewa dole a sanya wata rana.

Ita kuma waccan kara da Hukumar DSS ta shigar a kotu ba a sanya ranar davza a fara sauratinta ba.

Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here