Daga Dr Magaji Dansarai
Idan mutane suka ninkaya cikin jin dadi da alfahari da daular duniya, to, babbar asarar da za su yi ita ce ta mutuwar zuciya da kara kwadayin abun duniya, har ma su mance da mutuncinsu.
Tawakkali zai bace masu ba tare da sun sani ba, ta yadda a koyaushe ba su tunanin komai sai dubarun samun abun duniya. Za su nutse cikin gasa da junansu har taimakon juna, ko hada kai wuri daya ya gagaresu, komi kalubalen da ke fuskantarsu, saboda kowane yana jin tsoron sadaukar da abun hannunshi don kada wani ya zarce shi. Munafunci da hassada za su yi kamari ta yadda kowa zai rika zargin dan’uwanshi, ko makwabcinshi, ko abokinshi.
In a ka kai ga haka, jama’a na ji, su na gani, bala’i da masiba za su dabaibayesu amma su kasa yin wani hobbasa don maganin abinda ya dame su. Manya da kanana, kowa tsoron ya rasa daular da ya ke ciki zai hana shi daukar matakin gyara rayuwar al’umma.
Abun takaicin, yanzu haka mu ke a Arewa. Mun yarda da kowane irin wulakanci ga mutuncinmu, ga addininmu, ga dukiyoyinmu da al’ummarmu domin so da mutuwar zuciya.
Duk wanda ya ke jin shi ya haye, don bala’in bai zo gareshi ba kai tsaye, to ya jira lokaci.
Idan Shugabanni za su kasa haduwa su taimaki talakawa, to ai wata rana ta su za ta same su.
Allah Ya yi mana jagora, kuma Ya jikan iyayenmu da rahamarShi, amin.














