Daga Isah Miqdaf
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, tare da hadin gwiwar shirin AGILE sun gyara makarantar Katsina Billingual School da ke SUNCAIS, a cikin Birnin Katsina.
Haka zalika, Gwamna Radda ya amince da sake farfado da Cibiyar koyan harshen Faransanci da za su ci gaba da gudanar da karatu a makarantar wanda za’a rika gudanar da shirin shaidar difloma da wasu kwasa-kwasai a cikin harshen Faransanci.
Cibiyar Koyon Harshen Faransanci da ke jihar Katsina a Najeriya, tana da fa’idodi da yawa na ilimi da suka hada da samun damar guraben karatu ga ɗaliban Katsina don yin karatu a Faransa, ba da darussa, bita, da takardun shaida cikin harshen Faransanci, adabi, da al’adu da kuma haɓaka sha’awar aiki a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, diflomasiyya da sauran su.
Haka zalika, wannan cibiyar za ta bada damar koyon harshen Faransanci da al’ada, haɓaka ƙwarewar sadarwa don dangantakar ƙasa da ƙasa, tafiye-tafiye, da kasuwanci.
Wannan kuduri ba karamin ci gaba zai kawo ba a harkar ilimi a Jihar Katsina ta dalilin kyakyawan Shugabanci na Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda