Gwamnatin Tarayyar Nigeriya ta jingine batun Karinn albashi da kingiuar Kwadagon Nigeriya ta fafutikar samau har sai Illa Masha Allah
Bayani haka ya fito NE daga Ministan Whatsapp Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Muhammad Idris a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labaran a fadar Gwamnatin Tarayya
game da shawarwarin da aka cimmaws yayin zaman Majalisar Zartaswar Nijeriya.
Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta jingine cigaba da naziri da tattaunawa akan batun sabon mafi karancin albashi domin baiwa Shugaban Bola Tinubu damar fadada tuntuba da masu ruwa da tsaki akan batun.
A cewarsa, shugaban kasar yayi nazarin rahoton da kwamitin nan mai bangarori 3 ya gabatar masa akan mafi karancin albashi kuma zai cigaba da tuntuba akansa kafin gabatar da matsayar karshe kan batun gaban Majalisar Dokoki.
An jima ana takaddama tsakanin Kungiuar Kwadagon da Gwamnatin Nijeriya akan mafi karancin albashin ga ma’aikatan gwamnatin Nijeriya.
Za a iya tuna cewa wa’adin dokar mafi karancin albashi ta 2019, da ta tsayar da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ya Kare a watan Afirilun da ya wuce. Bisa waccan Dokta Wagini ne a rika sabunta dokar duk bayan shekaru 5 domin dacewa da bukatun tattalin arzikin ma’aikata na wannan lokaci.

I’mA watan Janairun da ya gabata Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori 3 domin tattaunawa akan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Kwamitin ya kunshi wakilan hadaddiyar kungiyar kwadago da na gwamnatocin tarayya dana jihohi da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.