Gwamnan Jihar Sokoto, Alh. Ahmed Aliyu ya ziyarci mahajjatan jJhar Sokoto da ke sansanin mahajjata a Mina tare da yaba musu akan irin yadda suka nuna dabi ‘u nagari a duk tsawon zaman u a kasar Saudiyya.
Gwamnan ya nuna farin cikin sa na ganin cewa babu wani mahajjacin jihar da aka samu ya nuna rashin da’a ko aikata assha, ko kuma yunkurin sabawa dokokin kasar Saudiyya.
Bayani haka na kunshi NE a wata takarar bayani ga manoma labarai Mai dauke da SA hannun Abubakar Bawa
Ya kara da cewa irin yadda mahajjatan suka kare martabar Jihar Sokoto da kasa baki daya babu shakka abin yabo ne kuma abin godewa tare da rokon Allah ya saka musu da alkhairi.
Gwamna Aliyu ya kara da cewa irin halaye nagari da mahajjatan jihar suka nuna ya sanya hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa, NAHCON sanya jihar a jerin jihohi da ke da mahajjata mafiya da’a da ladabi da biyayya.
Saboda haka Gwamnan ya bukaci mahajjatan da su dore da irin wadanan halaye a lokacin da suke kasa mai tsarki da gida Najeriya, yana Mai tunatar da mahajjatan cewa suna a kasa mai tsarki ne inda ke da wurare da ake saurin karba addu’a Don haka su dage da yi wa kasar nan addu’a don fita daga dimbin matsaloli da suke yin kafar ungulu wajen ciyar da ita gaba.
Bugu da kari,Dr Ahmed ya kuma bukace su da su saka Jihar Sokoto a addu’oin su domin neman agajin Allah akan matsalar ‘yan ta’adda da suka hana wasu yankunan jihar samun zaman lafiya.
Gwaman ya kara bada tabbacin cewa gwamnatinsa a tsaye ta ke kyam don kawo karshen rashin tsaro, tare da tabbatar da kare rayukka da dukiyoyin alummar jihar,
Haka ma Gwamnan ya kara baiwa mahajjatan tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da jin dadinsu a daidai lokacin da suke dakon soma jigilarsu zuwa gida Najeriya.
Gwaman ya kuma leka a tentunan alummar yankin mulkin Gada inda ya yi taaziyya akan rasuwar wani mahajjaci dan yankin tare da rokon Allah ya gafarta masa.
Haka ma gwamnan ya leka tentunan kananan hukumomim Wamakko da Tambuwal inda ya duba wasu marasa lafiya tare da fatar Allah ya tashi kafadunsu.
A karshe kuma gwamnan ya yi godiya ga daukacin mahajjatan jiha akan irin goyon baya da suke baiwa humumar jin dadin alhazzai ta jihar Sokoto, abin da ya ce ya taimaka gaya wajen samun nasarar da aka yi.
A lokacin ziyarar dai gwamnan na tare ne da rakiyar Kakakin m
Majalisar Dokokin jiha kuma Amirul Hajj,Tukur Bala Bodinga,da Sakataren Gwamnatin jiha, Muhammad Bello Sifawa, da shugaban Ma’ikata a fadar gwamnatin jiha Aminu Haliru Dikko da Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jiha Aliyu Musa da kuma wasu daga cikin manyan jami’an