Nasarorin Gwamna Radda cikin kwanaki 10a0

705

Bayanin aikace-aikace da nasarorin da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ya cimmawa cikin kwanaki 100 da karbar ragamar tafiyar da Jihar Katsina a matsayin Gwamna

1. Gudanar da shirin tantance ma’aikata domin tabbatar da sahihancin yawan ma’aikatan gwamnatin da jihar ke da su.

2. Rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta kudin da suka kai Dalar Amurka milyan 13 da Shirin Raya Kasashe na Majalisar Dinkin Duniya UNDP domin kafa cibiya ta musamman don kare yankin arewa maso yammacin Nijeriya.

3. Sa hannu kan kudiurin dokar kafa asusun bai-daya na TSA a Jihar Katsina.

4. Hadin guiwa da Bankin Musulunci don inganta aikin gona, ilmi da samar da ayyukan raya kasa.

5. Fitar da Naira milyan 112.5 don ba da tallafin karatu na ‘Scholarahip’ ga dalibai ‘yan asalin Jihar Katsina da ke karanta kwasa-kwasan da suka shafi kiwon lafiya su 546 ‘yan shekarar 2023 da ke karatu a ciki da wajen Nijeriya.

6. Gabatar da kudurin doka da ke neman a kafa wata cibiya ta musamman da za ta inganta taswirar Jihar Katsina ‘KATGIS’.

7. Amincewa da kafa jami’ar kiwon lafiya ta Gwamnatin Tarayya a shiyyar Funtua, da za ta samu mazaunin didindin a karamar hukumar Funtua,har Katsina.

8. Ginawa tare da fadada magudanan ruwa a gadar kurde ta Kofar Kaura ‘Underpass’ cikin birnin Katsina.

9. Daukar matasa 2,400 a aikin samar da tsaro a yankunan jihar Katsina karkashin shirin ‘Katsina Community Watch Corp’.

10. Daukar aikin dindindin na malaman S-POWER su 7,000 a makarantun firamare da sakandare na fadin jihar Katsina.

11. Gabatar da kudirin doka ga majalisar dokokin jihar Katsina don neman kafa hukumar kula da kanana da matsaikan masana’antu a jihar.

12. Rabon kudin tallafi Naira milyan 20 don agaza wa iyalan ‘yan sintirin Vigilante da suka rasu a lokacin da suke a bakin daga don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina.

13. Kokarin hada hannu da Cibiyar Wellcome Sanger da ke Cambridge, Ingila domin kafa cibiya ta musamman da za ta dakile yaduwar cutuka masu yaduwa a jihar Katsina.

14. Jarabawar gwajin inganci ga manyan sakatarori ‘Permanent Secretaries’ 36 a jihar Katsina wadda irinta ce ta farko tun da aka kirkiri jihar domin zakulo hazikan manyan ma’aikatan da za su tafiyar da lamurran gwamnatin jihar.

15. Gabatar da kudirin doka ga majalisar dokokin jihar Katsina domin neman kafa Cibiya ta musamman da za ta taimaka wajen inganta tsaro a lungu da sako na jihar wato ‘Katsina Community Watch Corp’.

16. Gudanar da jarabawa domin zakulo hazikai daga cikin malaman makaranta na wucin-gadi su 693 a ma’aikatar kula da ilmin firamare da sakandare ta jihar domin a ba su aikin dindindin.

17. Kafa ma’aikatar kula da harkokin tsaro da lamurran cikin gida.

18. Ba da aikin gwamnati ba tare da bata lokaci ba ga dalibai ‘yan asalin jihar Katsina da suka yi zarra wajen karatunsu a jami’ar Musulunci ta Bangladesh.

19. Amincewa da fitar da kudi Naira bilyan 2.7 domin gina makarantun sakandare 75 karkashin shirin inganta ilmin ‘ya’ya mata na AGILE, wanda hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Katsina da Bankin Duniya.

20. Rarraba babura 198 domin zagayen rigakafi ga jami’an da ke gudanar da aikin wanda shiri ne hadin guiwa da GAVI da UNICEF.

21. Ba da gudunmuwar kudi N100,000,000 ga Gidauniyar Atta’awlu Foundation. (N68,000,000.00 daga kananan hukumomi 34 na jihar, sai gwamnatin jiha ta ba da N32,000,000) domin gina cibiyar kula da ‘yan gudun hijra, marasa karfi da marayu a jihar Katsina.

22. Kafa kwamitin da zai zakulo masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar Katsina.

23. Sayowa tare da rarraba buhunan hatsi 100 ga kowace mazaba 361 da ake da su a jihar Katsina.

24. Samar da fili mai fadin kadada 76.40 domin fadada filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina domin ya zamnto ya cimma tsara a idon duniya.

25. Biyan diyyar kudi Naira milyan 300 ga mutane 421 da ke da filaye a kusa da filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua Katsina da aka yi amfani da filayensu don fadada filin jirgin.

26. Ziyara a ma’aikatar kula da muhalli ta kasa domin shawo kan matsalolin da suka jibinci muhalli a jihar Katsina.

27. Kafa Cibiyar alkinta bayanai da sadarwar zamani ta ICT a jihar Katsina.

28. Gudanar da addu’o’i na musamman domin samun ingancin tsaro a jihar Katsina da shirye-shiryen fadakarwa ga malaman addini musamman kan lamarin da ya shafi hambarar da gwamnatin Bazoum da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.

29. Kafa sashen farfado da aikin gwamnati a jihar Katsina.

30. Kafa Cibiyar horar da kwallon kafa mallakin jihar Katsina.

31. Amincewa don sayo kayan aikin jami’an tsaro na kudi Naira bilyan 7.8 don inganta tsaron lungu da sakon jihar Katsina.

32. Amincewa a sayo karin motocin safa-safa guda 40 kan kudi Naira milyan 600 don sufuri a hukumar KTSTA tare da tallafar daliban firamare da sakandare wajen zuwa makaratunsu cikin sauki.

33. Kafa kwamitin da zai zana taswirar yadda za a aiwatar da Asusun bai-daya na TSA a jihar Katsina.

34. Amincewa da horar da daukacin ma’aikatan gwamnatin jihar Katsina kan yadda ake amfani da na’ura mai kwakwalwa ta ‘Computer’.

35. Rarraba buhunan shinkafa 40,000 ga masu karamin karfi a fadin jihar Katsina domin rage musu radadin tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur ya jawo.

36. Ba da kudi Naira milyan 271 domin sayo kayan koyo da koyarwa a rarraba su a daukacin makarantun firamare da na sakandare na jihar Katsina.

37. Kaddamar da kwamitin tsarin inganta yadda za a rika kashe kudin gwamnatin jihar Katsina.

38. Ginawa tare da gyaran famfunan tuka-tuka da makewayai a kananan hukumomin Batagarawa, Katsina, Daura, Baure, Funtua da Kafur.

39. Gina rijiyoyin burtsatsai masu amfani da hasken rana da makewayai a makarantu 15.

40. Ginawa tare da gyaran rijiyoyin burtsatsai masu amfani da hasken rana a cibiyoyin kiwon lafiya 10 a jihar Katsina.

41. Sakar wa kananan hukumomi kudi Naira bilyan 1.8 domin su gudanar da ayyukan raya kasa.

42. Sayo makamai na kudi Naira bilyan 1.2 a matsayin gudunmuwa ga jami’an tsaro a jihar Katsina.

43. Duk wata ana ba kananan hukumomi Naira milyan 10 domin su rika tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

44. Dauka tare da horar karin ‘yan sintirin Vigilante 150 a kowace karamar hukuma don inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina.

45. Sayo mota kirar Toyota Hilux da babura a kananan hukumomin Kaita, Charanci da Danmusa domin inganta tsaron kananan hukumomin.

46. Biyan alawus-alawus na jami’an tsaro, kula da kayan aikinsu musamman motocinsu masu sulke na APC da sauran ababen hawan jami’an tsaro.

47. Amincewa a sayo motoci masu sulke guda 10 da motoci kirar Toyota Hilux guda 65 sai babura 700 kan kudi Naira bilyan 5.4 don tallafar ayyukan jami’an tsaro a jihar Katsina.

48. Rarraba kayan jin kai na Naira milyan 11,300,000 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa su 265 a Sabuwar Unguwar Dutsin Amare da Tudun Katsira a cikin kwaryar birnin Katsina ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA.

49. Rarraba kayan aiki a asibitoci a cibiyoyin kiwon lafiya na Kofar Kaura, Asibitin Turai, Asibitin Kwado, asibitin Abukur da Asibitin Dangani da na garin Radda a jihar Katsina.

50. Rarraba kayan aikin noman rani ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA.

51. Rarraba kayan jin kai na Naira milyan 46 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa su 611 a kananan hukumomi 7 da suka hada da Katsina, Batagarawa, Daura, Dandume, Mani, Musawa da Charanci.

52. Rarraba kayayyaki ga mutane 5600 daga kananan hukumomi 22 a jihar Katsina shirin hadin guiwa dauki na musamman daga gwamnatin tarayya ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022.

53. Ba hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina ‘yancin cin gashin kanta.

54. Sake sanya bututun ruwa na Pipe-pipe a wurare daban-daban wanda aikin hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Katsina da shirin SURWASH domin samar da ruwan sha a garin Tsanni cikin karamar hukumar Batagarawa, sai Batagarawa Low Cost, rukunin gidaje na Sardauna Estate, Tudun Matawalle, Ambassador Quarters, Tayoyi, Kofar Guga, Kofar Yandaka da Rafindadi.

55. Ginawa tare da gyaran tsarin samar da ruwan sha na garin Musawa.

56. Ba da kwangilar gyara da daga darajar wuraren samar da ruwan sha na garuruwa Dutsinma, Malumfashi, Funtua, Daura da Katsina.

57. Sa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da cibiyar samar da ayyukan ci gaba ta kasa domin inganta hanyoyin samar da ruwan sha daga dam din Zobe a yankunan Safana da Danmusa. Kazalika, akwai wani kason na aikin inganta samar da ruwan shan a garuruwa ln Dutsinma, Karofi, Radda, Kafinsoli, Tafashiya da Kankia.

58. Kawo wani kamfani daga kasar China domin inganta hanyoyin samar da ruwan sha a jihar Katsina ta hanyar samar da tsayayyen lantarkin da ake bukata.

59. Gabatar da kudirin doka ga majalisar dokokin jihar Katsina da ke neman a kafa hukumar kula da masu noman rani a jihar.

60. Gabatar da kudirin Doka da ke neman a kafa hukumar kula da ci gaban jihar Katsina. Aikin hukumar dai shi ne ta saka idanu kan duk wasu ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a jihar da kokarin shiga tsakani wajen duk wata hadin guiwa da ake son yi tsakani wani bangare da jihar Katsina da kuma tabbatar da an yi raba daidai wajen rabon abubuwan bukata domin samun ci gaba mai dorewa.

61. Akwai kudirin doka na neman a yi gyaran fuska ga dokar da ta kafa hukumar tattara haraji ta jihar Katsina ta 2021. Kudirin dokar na neman a yi garambawul domin habbaka samar da kudaden shiga, tabbatar da ana biyan haraji da kuma tabbatar da sa ido kan harkokin kudi.

62. Kaddamar da kwamitin da zai duba yadda za a aiwatar da shirin inganta fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi a jihar Katsina.

63. Kaddamar da kwamitin da zai bincika ya gano gandayen dajin da aka ba da a matsayin gonakin noma a jihar Katsina.

64. Ziyarar zuwa cibiyar nazarin harkokin tsaro ta kasa da zummar kulla kyakkyawar alaka da cibiyar don kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar Katsina.

65. Kaddamar da kwamitin da zai lura da daukacin yadda za a dauki matasan da za su taimaka wajen inganta tsaro a shirin Katsina Community Watch Corp’ da Manjo Janar Junaidu Bindawa ke jagoranta.

66. Ziyarar hedikwatar tsaro ta kasa, Abuja a inda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ya gana da hafsan hafsoshin Nijeriya inda suka tattauna batutuwa daban-daban da ke da nasaba da yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da wasu yankunan jihar Katsina ke fama.

67. Sa hannu kan wasu dokoki da suka shafi tsaro a jihar Katsina. Dokokin sun hana zirga-zirgar mutane a kan baburan haya da Keke napep daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a kananan hukumomi 19 da ke fama da matsalolin tsaro.

68. Kaddamar da shirin VSF na 2023 domin inganta rayuwar al’umma da tallafar yankuna.

69. Ba da gudunmuwar kayan aiki ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kauyen Dangani da kuma tallafar dakin shan magani na kauyen Dangani da kayan aiki.

70. Ba da gudunmuwar hatsi ga ‘yan gudun hijra a yankin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

71. Gina rijiyar burtsatse domin samar da wadataccen ruwan sha a ma’aikatar kula da Ilimin firamare da sakandare ta jihar Katsina ta tallafin shirin AGILE.

72. An gudanar da bincike mai zurfi kan tsarin aikin manyan darakatocin ma’aikatar ilmi da jami’an kula da ilmi na shiyya a ma’aikatar kula da ilmin firamare da sakandare ta jihar Katsina domin karfafa musu guiwar aiki yadda ya kamata.

73. Wata hadin guiwa ta musamman tsakanin masu ruwa tsakin jihar Katsina da Bankin duniya da kuma kungiyar gwamnonin Nijeriya a bangaren ilmi.

74. Gudanar da bita ta kwanaki uku ga masu ruwa da tsaki kan shirin inganta ilmi na shekara-shekara.

75- Kafa sashe na musamman domin kula da Wanda ibtila’i na yan ta’adda ya fadamawa da kuma yan gudun hijira.

76-Rage kudin sufuri da hukumar sufurin jihar Katsina ta yi don zirga-zirgar cikin jihar.

77- Cikakken nazari akan wa’adin dukkan ma’aikatu da hukumomi domin kawar da kwafi da rashin wadatuwa a jihar.

78- Kafa ma’aikatar ilimi mai zurfi.

79- Kafa Hukumar Kula da Kadarorin Jihar Katsina.

80- Aza harsashin ginin cibiyar wankin koda mai gadaje 16 a Katsina da Funtu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here