Gwamna Radda ya rantsar da sabon sakataren gwamnati

1076

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar (SGS) Barr Abdullahi Garba Faskari a gidan gwamnati, da ke Katsina.

Nadin Barr Abdullahi Garba Faskari a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya zo ne bayan Arch Ahmad Musa Dangiwa ya yi murabus daga mukamin, bayan da ya samu mukamin minista a Gwamnatin Tarayya.

Malam Dikko Umaru Radda a lokacin bikin rantsuwar ya ce nada Barr Abdullahi Garba Faskari ya biyo bayan samunsa da kwarewa da gogewa da aiki tukuru da dattakun da duk ake bukata ga aikin hidimta wa al’umma.

Mai Girma Gwamnan ya bukaci sabon Sakataren Gwamnatin da ya yi amfani da irin basira da gogewar da ya ke da ita wajen ganin jihar ta ci gaba.

Gwamna Radda ya ce Barr Abdullahi Garba ya aminta zai hidimta wa Jihar Katsina a matsayin Sakataren Gwamnati ba tare da ya yi la’akari da mukamin mataimakin Gwamna da ya taba rikewa ba, sai don ya hidimta wa Jihar Katsina.

Bikin rantsuwar ya gudana ne akan idon mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruq Lawal Jobe, Babban Jojin jiha Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, Alkalin Alkalai na jiha da ‘yan majalisar zartarwar jihar Katsina.

Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here