A tallafawa marasa karfi – Gwamna Masari

511
Daga Lawal Gwanda, Katsina
An bbukacii jammaa’a, mmusamman mawaada, d su rika tallafawa masu karamin karfi a cikin al’umma.
Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan kira a lokacin kaddamarwa da kuma raba kayan aikin asibitin ƙashi dana sauran asibitoci, litattafan karatu, kekunan tura marasa lafiya guda 100, da sauran kayan kula da lafiyar yara da gidauniya Aminu Masari Foundation tare da hadin gwiwar kungiyar Bruderlife suka  shirya.
An gudanar da taron  a dakin taron shugaban kasa da ke Gidan gwamnatin Jihar Katsina.
 Ya ce gidauniyar da aka assasa kimanin shekaru 18 da suka gabata, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimaka ma mabuƙata musamman akan abubuwan da suka shafi ilimi da makamantansu.
A nashi ɓangaren, shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Kabir Mashi wanda ya samu wakilcin mataimakinshi Abdullahi Imam ya yi kira ga mutanen da ke da niyyar bada gudunmawarsu zuwa ga mabuƙata da su bada ta ta hanyar gidauniyar.
Tunda farko a jawabinshi sakataren gidauniyarAlh  Ibrahim Ahmed Katsina, ya ce gidauniyar na gudanar da ayyukan taimakon al’umma daban daban da suka shafi aikin idon da aka yi ma kimanin mutane 100 a fadin Jihar Katsina a baya.
Ya ce hakan dai kari ne ga taimakon kiwon lafiya da aka ba mutane 3,000, inda yake mai bayyana cewa a kwanakin baya ma gidauniyar ta taimaka ma mutane masu bukata ta masamman da kekuna 200.
Itama da take magana, ma’assasiyar kungiyar Bruderlife Mrs. Merry Bruder ta yaba ma gidauniyar Masarin bisa yin haɗin gwiwa da su, tare da aiwatar da shirye shirye masu amfani ga rayuwar al’ummar Jihar Katsina.
Ta kum yaba ma Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zakiyya Aminu Masari bisa taimakon da ta ke ba kungiyoyi masu zaman kansu don ganin sun yi aiki a jihar.
   Shugaban hukumar gudanarwar Asibitin Katsina Dr. Abduljalal Umaru Abdullahi da kuma mai ba gwamna shawara akan masu bukata ta masamman Ya’u Rufa’i Zakka sun yi alkawarin yin amfani da kayan yadda ya dace.
Hakanan kuma mai ba gwamnan shawara ya bukaci gwamna da ya hanzarta amincewa da kudirin dokar kafa hukumar gyare gyare wanda yanzu haka ya ke gaban majalisar dokokin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here