ANA ta yi tir da kiran cire Sanata George Akume

779

Kungiyar ANA, Arewa New Agenda, ta yi fatali da kiran a cire Sanata George Akume daga mukaminsa na Sakataren Gwamnatin Tarayya.

ANA dai kungiya ce da ke fafutikar tabbatar da zaman lafiya, musamman a Areawacin Nijeriya.

Kungiyar ANA a karkashin jagorancin Sanata Ahmad Abubakar MoAllahyidi, ta nuna damuwa tare da bakin ciki game da wadannan kiraye- kirayen cire Sanata Akume daga mukaminsa da wasu ‘yan siyasa ke yi.

Chief Audu Ogbe

Babban abin da ya damu ANA shi ne wata sanarwa ga manema labarai da Cif Audu Ogbe ya bayar a wani taron manema labarai a lokacin da ya jagorancin manyan kabilar Idoma yana mai nuna rashin gamsuwa da matakan da Sanata Akume ya dauka game da bayar da mukamin minista daga kabilar Tiv, tare da yin korafin danne kabilar Idoma.

ANA ta ce ta fahimci cewa Cif Audu Ogbe da mukarrabansa suna da ‘yancin bayyana ra’ayinsu akan kowace harkar siyasa amma ta damu ainun akan zargin cewa an bayar da sunan wanda za a nada akan mukamin minista don a danne ‘yan kabilar Idoma tare da dora laifin akan Sanata George Akume.

ANA ta ce wannan zargin yana iya sanyawa mutane mugun tunani a zukatansu.

SanatAhmad Abubakar MoAllahyidi Shugaban ANA na Kasa

 Bayanin ANA ya ce ‘ yan Nijeriya daga dukkan sassa sun yi maraba da nadin Sanata Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya sabida ganin haka ya daidaita tsarin rabon mukamai a Nijeriya bayan kammala zabukan 2023.

An nada Sanata Akume ne domin Arewa da Kiristoci su samu wakilci a Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, in ji ANA tana mai jaddada cewa nadin Sanata Akume ya wuce siyasar Jihar Binuwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here