Gwamna Radda Ya Kaddamar da Motocin Sulke

687

Daga Isah Miqdad

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya mika wa jami’an tsaro motocin yaki masu sulke guda 10 domin gudanar da aiki a kananan hukumomi 8 da ke fama da matsalar  tsaro.

Wannan gagarumin taron kaddamarwar ya gudana ne a ranar Litinin, 15 ga Afrilu, 2024 a gidan gwamnatin jihar Katsina.

A nasa jawabin, Gwamnan ya jaddada cewa ya bi sahun sa na ganin an samar wa hukumar tsaro ta Katsina Community Watch Corps da ‘yan Sanda, sojoji da duk wani abu da ya dace domin fuskantar matsalar rashin tsaro a jihar Katsina. Ya bayyana cewa, a lokacin yakin neman zabensa, ya yi alkawarin samarwa al’ummar jihar Katsina muhimman dabarun tabbatar da tsaro. Ya kuma mika godiyarsa ga hukumar Katsina Community Watch Corps da sauran jami’an tsaro bisa irin nasarorin da suka samu.

Kodayake ya ce ba za a ce an kawar da rashin tsaro gaba daya a jihar ba, ya tabbatar wa da al’ummar Jihar cewa an samu gagarumin ci gaba kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen samar da zaman lafiya a jihar Katsina.

An ware motocin ne ga kananan hukumomi takwas na gaba-gaba dake fama da rashin tsaro da suka hada da: Safana, Batsari, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume, da karamar hukumar Jibia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here