APC ta  rusa Kwamitin mansu ruwa da tsaki a Katsina

526

Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina ta rusa kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin jiha da kananan hukumomi. Mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Bala Abubakar Musawa ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina.

Da ya ke jawabi a madadin shugaban jam’iyyar na Jihar Katsina, Alhaji Sani Ali Daura, mataimakin shugaban ya jaddada cewa rusa su zai fara aiki nan take. Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta fito da hanyoyin da za a bi wajen sake kafa mambobin kwamitocin masu ruwa da tsaki, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Wani bayani daga Isah Miqdad, mai taimakawa Gwamna Radda a harkokin jar idu na zamani ya ambato Alhaji Abubakar Bala yana yabawa masu ruwa da tsaki masu barin gado bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabukan da suka gabata, yana mika sakon taya murna bisa ga gudunmuwar da suka bada kuma ya nemi fahimtarsu da gaske tare da yi musu fatan alheri a harkokin siyasarsu na gaba.

Bugu da kari, shugaban ya bada tabbacin cewa za’a gudanar da zaben sabon kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakin jiha da kananan hukumomi cikin adalci da adalci.

Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here