Gwamna Radda ya kaddamar da aikin hanyoyin Birnin Katsina

752

Gwamnan Dikko Radda na Jihar Katsina ya kaddamar da fara ayyukan fadada habyoyin cikin Birni Katsina.

Bikini kaddamar da ayyukan ya gudana ne a ranar Laraba yay in da Gwamnan Dikko ya kaddamar da akin titin Kofar Soro zuwa Kofar Guga zuwa tagwayen hanyoyi a cikin birnin Katsina.

A lokacin da ya ke jawabin kaddamar da fara aikin, Gwamna Dikko Radda, ya fara da bayyana makasudin yin aikin domin kara daga darajar birnin Katsina wanda ya kasance gari mai tsohon tarihi ba a Najeriya ba har ma adaukacin Yammacin Afirka, wanda kuma idan an kammala aikin zai haɓaka kasuwanci, da kuma inganta rayuwar al’ummar yankin.

Aikin fadada hanyar wanda zai lakume kimanin Naira Biliyan Uku da Rabi (N3,550,000,000) wanda ya hada da hanyar da ta taso daga Galadanci ta bi ta gidan Hassan Usman Ciroma, zuwa Central Police Station (CPS) tare da sanya fitilu masu amfani da hasken rana, tare da biyan kudin diyya ga al’ummar da aikin ya shafi muhallin su.

Kamfanin “Mother Cat ” ne zai gudanar da aikin. Shugaban kamfani ya yi alkawarin gama aikin cikin kasa da watanni goma sha takwas (18) da aka ba su.

Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Faruq Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura; Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri; Yan Majalisar Zartaswa na Jihar Katsina, Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Aminu Ashiru; Babban Jojin Jihar Katsina, Justice Musa Danladi Abubakar, da sauran su.

Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here