EFCC ta mayar da Murtala Nyako zuwa kotu

647

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Murtala Nyako da dansa Abdulaziz a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis bisa zargin almundahanar Naira biliyan 29.

An sake gurfanar da su a gaban kuliya bisa laifuka 37 da ake zargin sun aikata a lokacin da Alhaji Nyako ke gwamnan Adamawa.

Sauran wadanda aka gurfanar da su akwai Zulkifik Abba da Abubakar Aliyu.

Kamfanonin da ake zargin sun yi amfani da su wajen karkatar da kudaden—Blue Opal Limited, Sebore Farms & Extension Limited, Pagoda Fortunes Limited, Tower Assets Management Limited, da Crust Energy Limited.

Hukumar EFCC na tuhumar Nyako, da dansa, da sauran wadanda ake tuhuma bisa zargin almundahanar kudi Naira biliyan 29.

EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun karkatar da kudade daga baitul malin Jihar Adamawa tsakanin watan Janairun 2011 zuwa Disamba 2014.

Warning: A non-numeric value encountered in /home/kunnenga/public_html/wp-content/themes/Newspaper/includes/wp_booster/td_block.php on line 1009

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here