Gwamna Radda ya samar da kwamitoci da za su dora Katsina kan kyakkyawan tsari

955

Gwamna Radda ya samar daGwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya kaddamar kwamitoci uku domin dora Jihar Katsina biss kyakkyawan tsarin da zai samar da ci gaban jihar.

Daga cikin  kwamitocin akwai na yadda za a aiwatar da tsarin asusun bai-daya na jiha, wato  TSA (Treasury Single Account) wanda ya kunshi wakilaii 12 a karkashin jagorancin Muhammad Aminu Isyaku da kuma Salisu El Ladan a matsayin Sakatare.

Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai yin bita ga tsarin asusun gwamnati da kuma tsara yadda sabon asusun na bai-daya zai yi aiki da sauransu.

Kazalika, akwai kwamitin inganta tsarin biyan fansho da garatuiti ga ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka ajiye aiki.

Kwamitin na da mambobi 12, da Dr Faruq Aminu a matsayin shugaba, sai Mukhtar Ammani a matsayin Sakataren kwamitin.

Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin, akwai binciko hakikanin yawan ‘yan fanshon da ake da su a halin yanzu tsakanin jiha da kananan hukumomi da bayar da  shawara ga gwamnati akan yadda za a kara inganta fansho a jihar Katsina da sauransu.

Sai kuma kwamitin da aka kaddamar don binciko gandun daji mallakin gwamnati, shi ma mai mambobi 12. Alhaji Khalil Bako ne zai jagoranci kwamitin da ofishin Gwamna a matsayin Sakatariya.

Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai gano gandayen dajin gwamnati da aka bayar domin gudanar da noma da yin bitar wadanda aka ba gonakin da sauransu.

Kwamitocin uku na da tsawon makonni hudu su gabatar da rahotaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here