Gwamna Dikko Radda ya rantsar da manyan sakatarori

1017

Daga Lawal Gwanda

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya rantsar da sabbin manyan sakatarori 36 domin gudanar da harkokin gwamnatinsa.

An gudanar da bikin rantsuwar

 a dakin taro na gidan gwamnatin jihar Katsina.

Babban Mai Talkadaea. Gwmna Radda akan harkokin watsa labarai Isah Miqdad,  a cikin wata takardar sanarwa ya ce sabon shugaban ma’aikatan jihar Katsina Alhaji Usman Isyaku ne ya fara shan rantsuwar kama aikin. Bayan rantsuwar da manyan sakatarorin suka yi, Malam Dikko Umaru Radda ya ce an nada su akan wadannan mukaman ne don an gano cewa sun cancanta bayan da suka ci jarabawar da aka shirya masu.

Gwamnan wanda ya ce ingantawa tare da bunkasa aikin gwamnati na daga cikin kududrori manya da gwamnatinsa ta sanya a gaba, ya taya su murna bisa wadannan mukamai da suka samu. Kazalika, ya yi kira gare su da su yi aiki kasa-rika domin sauke nauyin da ya rataya kansu.

Ya ce da irin gogewar da suke da ita, Jihar Katsina na bukatar su ba da dukkan gudunmuwa don kakkabe kalubalen da jihar ke fuskanta, musamman bangaren tsaro da na kokarin tattara kudaden shiga.

Malam Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatinsa a kodayaushe tsaye take wajen ganin ta kyautata wa al’ummar Jihar Katsina domin su ci ribar. dimokradiyya.

Bikin rantsuwar ya samu halartar iyalai, abokai da masu fatar alheri ga sabbin manyan sakatarorin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here