Yada labarun karya akan Bola Tinubu

971

Daga Abdulaziz Abdulaziiz: Mun lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook suna yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda suke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Wannan magana ƙarya ce tsagwaronta wanda maƙiya suka shirya domin bata sunan  Ahmed Bola Tinubu.

Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su waɗannan masu yaɗa labarun ƙarya suka dogara da ita wajen ruwaito wannan magana ta bogi.

Muna Jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zaɓe, ƴan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta koƙarin yaɗa labaran ƙarya da sharri domin ɓata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayar da da su a akwatin zaɓe ba sai sun haɗa da ƙarya da sharri domin ɓata musu suna.

Ɗan takarar jam’iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha faɗar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zaɓe ba. Abin da muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zaɓin ɗan takarar da suka ga ya dace kuma yana da ƙwarewar aiki da zai iya kawowa ƙasa cigaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen rudar da tunanin masu zaɓe.

Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin bogi marar hujja wanda wasu maƙiya kuma marasa son zaman lafiya zuka ƙirƙira.

Abdulaziz Abdulaziz

Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here