Faransa za ta janye sojojinta daga Nijar

630

Faransa ta bayyana cewa za ta janye sojojinta da ke girke Jamhuriyar Nijar bayan kwashe kimanin watanni biyu ana takin-saka tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, watao bayan juyin mulkin da aka yi wa gwamnatin Mohammed Bazoum.

A ranar Lahadi ne aka ruwaito Shugaban Faransa Emmanuel Macron yana bayani ga wata tashar talbojin cewa Fadansa za ta janye dakarun da ta girke a Nijar ya zuwa karshen wannan shekaru kuma jakadanta da ke kasar zai koma gida.

Tun farko hukumomin Nijar sun bayar da umurnin Faransa ta janye sojojinta daga Nijar, ta kuma yanke hulda da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu, amma Faransa ta yi watsi da wadannan bukatu har tana cewa gwamnatin sojan haramtacciya ce kuma ba ta hurumin yin wadannan hukunce hikunce.

A lokacin da Nijar ta bukaci jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar, Faransa ta fiti karara ta ce ba zai fita ba.

Ya zuwa yanzu Faransa ta bayar da kai bori ya hau kuma Gwamnatj da jama’ar Nijar suna murna da wannan sabon mataki.

Nijar dai tana cikin kasashen da Faransa ta yi wa mulkin malla kuma har kafin wannan juyin mulki suna shan azabar mulkin malla a hannun Faransa domin ita ke gudanar da komi daga yanke hukuncu- hukuncen siyasa da tattalin arziki ta hannun ‘ yan Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here