Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da ginin makarantar Dimorkul

788
mGwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya kaddamar da ginin makatarantar Dimorkul a yankin Karamar Hukumar Mai’aduwa da ke shiyyar Daura ta Jihar Katsina.
Makarantar Dimorkul na cikin makarantu uku na musamman, wato daya a kowace mazabar Majaliasr Dattijai da Gwamna Dikko Radda ya yi alkawarin ginawa a lokacin yakin neman zabensa
Mai Girma Gwamnan ya bayyana garin Dimorkul a matsayin mai dumbin tarihi ba ma a jihar Katsina kadai ba, har a Nijeriya baki daya.
A yayin bikin kaddamar da ginin makarantar, Malam Dikko Radda ya ce za a gina ta ne domin ‘ya’yan talakawa kuma za a wadata ta da dukkanin abin da ake bukata na koyo da koyarwa. Yin hakan na nufin dan talaka ya samu ilmi mai inganci kamar yadda ‘ya’yan masu hannu da shuni ke zuwa makarantu masu inganci.
Mai Girma Gwamna ya yi addu’ar Allah Ya kawo ingantaccen tsaro a jihar Katsina da dawwamammen zaman lafiya domin kowa ya koma harkokinsa yadda ya kamata.
 Wadanda suka halarci aza harsashen ginin makarantar sun hada da Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar; Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Sani Aliyu Daura; Danmadamin Daura, Alh. Musa Haro da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here