Tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina ke gabanmu  – Gwamna Radda

786

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya ce babu abin da gwamnatinsa ta sa a gaba kamar tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummabna lungu da sako  kamar yadda suke rayuwa a baya.

Gwamnan ya kara jaddada shirin gwamnatinsa na hada hannu da hukumomin tsaro da ke jihar domin ganin tsaron al’ummar jihar ya inganta.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin takardar sanarwa ga manema labarai da Isaj Miqdad yanyawa hannu kuma raba ga manema labarai a Katsina.

Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin babban Sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 14 da ta hada Katsina/Kaduna AIG Ahmad AbdurRahman a lokacin da ya ziyarci Gwamnan a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Gwamnan ya yi la’akarin cewa babu inda ke samun ci gaba muddin tsaron yankin na samun tazgaro. Ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta hada hannu da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin ganin Katsinawa sun koma harkokinsu yadda ya kamata ba tare da wata barazanar tsaro ba.

Ya bukaci hadin kai da goyon bayan jami’an tsaron wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Mataimakin Babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta 14 ya jinjina wa Gwamnan ganin yadda a kodayaushe ya ke tsaye wajen ganin an tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina tun lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamna a watan Mayun, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here