Gwamna Masari ya yi ban- kwana da Katsinawa

942

Gwamnan Jihar Katsina, Alh Aminu Bello Masari ya bukaci jama’ar Jihar Katsina da su baiwa gwamna msi jiran gado, Dokta Dikko Umar Radda goyon baya fiye da wanda suka ba shi domin Jihar Katsina ta samu karin ci gaba.

Gwamna Masari ya fadi haka ne a lokacin da Kungiyar Dattawan Jihar Katsina (Katsina State Elders Forum) ta kai mashi ziyarar bankwana, a fadar gidan Gwamnati.
Masari ya ci gaba da cewa “Dokta Dikko Umar Radda danku ne, kuma shi ma  dan Jihar Katsina ne, yanzu shi ne wanda zai gaje ni, saboda haka ina rokon ku da ku bashi goyon baya fiye da wanda kuka bani, kana ku rika bashi shawara ba tare da gajiyawa ba domin ciyar da Jihar Katsina gaba.
Gwamna ya ci gaba da cewa babu abin da ya fi mahimmanci ga Shuganci fiye da mutunta al’umma da sanin darajarsu da kuma ba kowa darajar da Allah (S.W.A) ya ba shi a matsayina na mutum. Wannan shi ne kyakyawan shugabanci.
Daga karshe Gwamna Masari ya yi masu godiya ta musamman akan irin shawarwari da cikakken goyon baya da suka ba shi yayin gudanar da shugabancinshi, haka kuma ya yi kira da su kara kaimi wajen hada kan al’ummar Jihar Katsina.
Tun a farko Shugaban Kungiyar Dattawan Alh Aliyu Balarabe wanda Alh Ali Sani, sakataren kungiyar ya gabatar da jawabi a madadin Shugaban, ya ce “babu abin da za mu yi sai yi ma Allah godiya da ya kawo karshen wannan mulki na Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari lafiya, duk da kalubalen da ya fuskanta amma ya samu nasarori masu tarin yawa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina.”,
Ya ce dole a jinjina wa Gwamna Aminu Bello Masari  tare da yaba mashi, a bisa ayyukan ci gaban kasa da ya shinfida ma Jihar Katsina, kama daga gyaran magudanun ruwa, gyaran makarantu da gina wasu, gyaran asibitoci, samar da cibiyar koyon aikin likitanci, gina hanyoyi, gina gadoji na kasa da sama guda ukku a cikin garin Katsina, samar da ruwan sha, da sauran wasu  muhimman ayyukan da lokaci ba zai bari mu ayyana su ba.
Ya ce daga Karshe suna mashi godiya tare da fatan alkhairi a madadin kungiya.
Shi ma a nashi Jawabin Mai Shari’a Sadiq Abubakar Abdullahi Mahut, Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, ya ce Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari Shugaba ne na gari, kuma abin koyi, wanda ba shi da wani buri da ya wuce cigaban al’umma. Saboda haka ya zama wajibi mu gode mashi , kuma zamu kasance masu yi maka addu’a Allah ya kara daukaka darajarka, kana zamu cigaba da yi maka biyayya.
Shi ma a nashi jawajin Alh Abubakar Danmusa ya ce kafin ya marama Masari baya, sai da ya gindaya mashi sharudda guda biyu. Na daya za ya gyara masu abisitin Garin Dan musa. Na biyu za ya gyara masu makarantar sakandare ta garin Danmusa. Ya ce duk Maigirma Gwamna ya ce ya dauki alkawari zai yi. Cikin yarda Allah bayan samun nasarar Masari, yau gashi duka alkawurran da ya daukar mani ya cika su, saboda haka da wannan sai mu taya shi murna , muna mashi fatan alkhairi.
Alh Abu Gidado tsohon minista, ya yaba ma Masari a bisa dattakunshi da karbar shawara da yake yi, haka kuma ya ce abin da ba ku sani ba shi ne duk watan azumi idan ya kama sai ya dauki nauyin ciyar da mutane 500 har azumin watan  Ramadan ya kare a masallacin Bilal Bin Rabah da ke Layout. Allah ya saka mashi da alkhairi.
Haka kuma wasu daga cikin dattawan anasu jawabin sun bayyana Maigirma Gwamna mutum Mai tausayi hakuri da juriya wanda wannan hakurin na shi ne ya sanya ya samu nasara a mulkinshi, muna mashi fatan alkhairi.
Daga karshe kungiyar ta roki Maigirma Gwamna da cewa Dan Allah idan an ba shi mukami a sabuwar Gwamnatin Tarayya to ya yayi hakuri ya karba domin ya ci gaba da ba al’ummarshi gudunmuwar da ya saba.
Wadanda suka halarci zaman sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina QS Alh Mannir Yakubu, Alh Muntari Lawal, Sakataren Gwamnati, Alh Idris Usman Tune, Shugaban Ma’aikata na Jiha, Alh Bature Umar Masari Shugaban Ma’aikata, da wasu daga cikin yan Majalisar Zartarwa, Alh Salisu Mamman Kadandani, CEO Continental Computers, da wasu daga cikin mataimaka na musamman na Maigirma Gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here