Al’ummar garin Sha Madara da ke karamar hukumar Daura sun bukaci Gwamna Dikko Umar Radda PhD da ya taimaka a kammala aikin samar da Ruwa na garin da gwamnatinsa ta fara amma aka yi watsi da shi
Wasu mazauna garin na Sha Madara Sa’idu Aliyu da Sabi’u Atiku sun yi bayanin cewa an qudurci gina rijiyoyin burtsatse guda goma da kafa tanki na karfe babba a sama da hada aikin da Solar panels da inverter wadanda ke gabatar da aikin ya wuce watanni ukku ku sama ko kasa sun daina zuwa wurin aikin.
Don haka ne suke bukatar Gwamna da ya bincika don kada a yi ma Gwmnati da Al’ummar garin na Sha Madara sakiyar da ba ruwa,watau Gwamnatinsa ta biya amma an bar su da karafa maras amfani.













