Dags Bature Mohammed
Harkokin tsaro sun inganta a Jihar Kaduna, musamman ganin wasu hanyoyi da wuraren da ba su biyuwa a da, yanzu ana shiga da fita ba tare da fargaba ba
Gwamna Uba Sani ya bayyana haka wajen taron kaddamar da Shugabannin hadakar matasan Arewa maso yamma da ya gudana a Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin gida, Barr Suleiman shayibu wanda ya wakilci Gwamna Uba Sani ya ce kafin zuwan Gwabna Uba Sani hanyar Birnin Gwari ba’a iya binsu sai ansa jami’an tsaro suna rakiya, amma yanzu duk wadannan hanyoyin ana binsu lafiya lau, masanman ma Birnin Gwari akwai kasuwannin da suka dade ba’a ci amma yanzu duk an bude su ana gudanar da harkokin kasuwanci a cikin su.
Gwamnan ya yabawa matasan da suka shirya wannan taron dan fadakar da junansu game da abinda ya shafi hadinkan matasa da kuma zaman lafiya.
Yayin da ya ke nasa jawabin Farfesa Khailani Muhammad Shugaban Hadakar Kungiyoyin APC na kasa ya gargadi matasan Arewa Maso Yamma mazansu da matansu kauracewa miyagun dabi’u.
Khailani Muhammad ya bayyana cewa Najeriya tana daga cikin kasashe masu arziki a duniya, amma sai matasa sun nisanci miyagun halaye, kamar kabilanci, shan kwaya, sata, da makamantansu sannan Allah zai azirtamu da Shugabanni na kwarai.
Ya bayyana matasa cewa sune kashin bayan kowace al’umma kuma sune manyan gobe.
Abin da muke bukata a Nijeriya shi ne shugabanni wadanda za su kula da yan Nijeriya wajen ba su tsaro, ingantancen illimi, kulawa da lafiyar ‘yan kasa, hanyoyi da sauran ababen more rayuwa.
Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta kara yawan JTF kuma ta inganta rayuwarsu ta wadata su da kayan aiki domi su taimakawa sojoji da ‘yan sanda wajen kare rayukan ‘yan Nijeriya.
Daga bisani hadakar kungiyar matasan sun karrama Farfesa Khailani Muhammad da lambar yabo a matsayinsa na Jajirtaccen dan kishin kasa mai taimakon matasa a fadin Najeriya baki













