Katsina za ta farfado da hadin gwiwa da Songhai don bunkasa Mairuwa, Dutsinma

615

Daga Isah Miqdad

GwamnanJihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar Songhai da ke Port-Novo, Jamhuriyar Benin a ranar Juma’a 26 ga watan Janairu, 2024.

Gwamnan ya samu kyakkyawar tarba daga Farfesa Nzamujo, shugaban cibiyar da ke ta fadi tashin ganin ta samu ci gaba ta kowane bangare.

Da isar Gwamna Malam Dikko  Radda da mukarrabansa, an zagaya da su lungu da sako na wannan cibiya da ta kasance a sahun gaba wajen inganta aikin gona.

Cibiyar Songhai ta kasance a kan gaba wajen ƙirƙira, musamman a fannonin aikin gona da na batun inganta yankunan karkara. Gagarumar gudunmawar da wannan cibiya ta bayar ga ci gaba mai dorewa abin yabo ne da gaske.

A yayin jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana cewa an kashe makudan kudade a cibiyoyin Songhai da ke kananan hukumomin Faskari (Mairuwa) da Dutsinma a jihar Katsina a lokacin tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema.

 Abin takaici, an yi watsi da waɗannan cibiyoyin tun shekaru goma da suka gabata. Don haka, makasudin ziyarar tasa shi ne nazarin yadda cibiyar ta samu nasara a Benin da kuma lalubo damar yin hadin guiwa.

Ya jaddada cewa babban makasudin shi ne a farfado da cibiyar a Katsina, domin baiwa matasa masu kishin kasa damar cin gajiyar wannan jari mai kima.

Gwamna Radda ya himmatu wajen neman hadin guiwa da cibiyar inganta cibiyoyin da ke Katsina, da nufin amfanar al’ummar Jihar Katsina.

A karshe ya bayyana cewa gwamnatin sa ta himmatu da kwazo wajen inganta fannin noma. Burin gwamnatin jihar Katsina ya wuce tabbatar da wadatar abinci domin ya hada da nufin samar da guraben ayyukan yi masu yawa ga al’ummar jihar da ke karuwa.

Tawagar Gwamna sun hada da Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Hon. Jabiru Tsauri; Kwamishinan noma, Farfesa Bakori; Babban makusancin Gwamna PPS, Hon. Abdullahi Turaji; Mai ba da shawara kan tattalin arziki, Hon. Khalil Nur Khalil; Darakta Janar na hukumar bunkasa zuba Jari ta Jihar Katsina Alh. Ibrahim Jikamshi; Darakta Janar na hukumar noman rani ta Katsina, Abdulkadir Nasir da sauran su.

Isah Miqdad,

SSA Digital Media to Katsina State Governor.

27/01/2024

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here