Gwamna Radda ya kaddamar da kamfanin Rano Air a Katsina

710

Cikin matukar farin ciki, Gwamna Radda ya kaddamar da jirgin kai tsaye a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina da yammacin ranar Lahadi, 21 ga watan Janairu 2024, inda ya jaddada kudirinsa na bude hanyoyin zuba jari da kuma inganta kasuwanci a Jihar Katsina.

A jawabinsa yayin kaddamar da jirgin, gwamnan ya bukaci mazauna jihar Katsina da masu sha’awar zuwa jihar da su yi amfani da wannan sabon tsarin sufuri, wanda a cewar shi wannan wani gagarumin ci gaba ne a harkar sufurin jihar.

Wadanda suka halarci bikin kaddamar da jirgin sun hada da Kakarkin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, Ministan Gidaje da Raya Birane, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa, Alh. Ibrahim Masari, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here