Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya bayyana bayar da mazauni domin fara koyarwa a sabuwar Jam’iar Ilimin Kiwon Lafiya da ke Funtua.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, a ofishinsa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, ranar Litinin, 8 ga watan Janairu 2024.
A lokacin ziyarar, Gwamna Dikko Radda ya bayyana wa Ministan Ilimi cewa tuni dai Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da Funtua Technical College a matsayin wurin da za ayi amfani da shi domin fara koyarwa a sabuwar Jami’ar Ilimin Kiyon Lafiya ta Tarayya da ke Funtua).
Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da bayarvda cikakken goyon baya ga Ma’aikatar Ilimi da kuma jami’ar wajen ganin an gudanar da aiki a cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma, Malam Dikko Radda ya bukaci al’ummar yankin Funtua da su ba da goyon baya da hadin kai domin samun nasarar fara koyarwa a jami’ar.
Farfesa Tahir Mamman a lokacin da ya ke jawabi, ya bayyana godiyar sa ga Malam Dikko Umaru Radda bisa ga irin yadda ya jajirce da kuma goyon bayan da ya ke ba Shugabannin wannan jami’a da kuma ita kan ta Ma’aikatar Ilimi, wanda a cewar sa yana bayar da muhimmiyar gudunmuwa don ganin an samu nasarar kafa wannan jami’a a Funtua.
Shi ma Sanata Muntari Dandutse ya bayyana cewa tuni dai suka ware wasu kudade a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 domin ganin cewa jami’ar ta fara aiki ba tare da samun tsaiko ba. Ya bayyana cewa Majalisar Dattijai za ta ci gaba da bayar da duk wata gudunmuwa ga jam’ar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A cikin tawagar mai girma gwamna, akwai Sanatan Shiyyar Funtua, Senator Muntari Dandutse, Shugaban Jami’ar, Professor BB Shehu, Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri, da kuma Alh. Shamsu Sule Funtua.













