Gwamna Radda ya nada mataimaka na musamman 25 kan yada labarai

363

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya amince da nadin mutane 25 masu amfani da kafar sadarwar zamani a matsayin masu taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da za a tura a ma’aikatu daban-daban na jihar.

Wannan matakin na da nufin kara fito da manufar Gwamnatin Dikko Radda na ba bangaren samar da bayanai muhimmanci sosai da yadda za a rika bayyana ayyukan da gwamnatin ke shimfidawa a cikin al’ummar jihar Katsina.

Bayanin nade-naden na cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai baies Gwamna Dikko Shawara akan harkokin kafafen yada labarai na zamani, Mal Isah Miqdad a ranar.

13 ga Nuwamba, 2023

Sanarwar ta ce za a dai tura sabbin wadanda aka nada din zuwa ma’aikatu sassa da hukumomin gwamnati domin su ba da ta su gudunmuwa wajen tabbatar an gudanar da gwamnati a saman faifai ta hanyar bayat da sahihan bayanan da ake bukata game da ayyukan wadannan ma’aikatu.

1. Shamsudeen Ashafa – Agriculture & Livestock

2. Sagir Ibrahim Rawayau-LGA Chieftaincy Affairs

3. Nasir Hassan Daudawa-Religious Affairs

4. Nura Adamu-Finance

5. Abdulrasheed Iliyasu Yandoma-Commerce, Trade & Investment

б. Aliyu Abubakar-Rural & Social Development

7. Jamilu Hashim Gora-Office of Deputy Governor

8. Muntari Umar-Water Resources

9. Falalu Lawal-Internal Security

10. Aisha Hamza-Environment

11. Hussaina Musa-Women Affairs

12. Said Surajo-Budget and Economic Planning

13. Bashir Ya’u- Basic and Secondary Education

14. Iliyasu Hannafi-Land and Physical Planning

15. Habib Ibrahim Doka-Special Duties

16. Zainab Adam Sambo-Health

17. Sadiya Sani Sadiq-Justice

18. Mustapha Rabiu-Youth and Sport Development

19. Usman Abubakar Danmusa-Higher Technical and Vocational Education

20. Alyasa’u Sabi’u-Information and Culture

21. Mustapha Ibrahim Kofar Marusa-Works and Housing and Transport

22. Abdullahi Salisu-SGS Office

23. Munirat Gwanda-Government House

24. Mubarak Hassan-Info-graphic Designer

25. Murtala Musaddat-Drone Camera Pilot

Da ya ke taya murna ga wadanda aka nada akan sabbin mukaman Gwamna Dikko Radda ya bukaci su sauke nauyin da ya hau kansu ta hanyar amfani da kwarewa da gogewa kan aikin ba da bayanai ta kafar sadarwar zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here