KATSINA: Ana tantance dalibai  domin tallafin karatun kasashen waje

467

Gwamnatin jihar Katsina ta fara tantance dalibai ’yan asalin jihar da suka yi nasarar cin jarabawar tallafin karatun kasashen waje (Foreign Scholarship).

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD a yunkurinsa na bunkasa ilimi a jihar, ya sake bullo da shirin bayar da tallafin karatu ga ’yan asalin jihar sama da 100 da za su yi karatun likitanci, ilimin fasaha da kuma Bio-economy don karatun digiri na farko a kasashen waje.

Mataimakin Gwamna Faruq Lawal Jobe wanda shi ne Shugaban kwamitin tantancewar, ya jaddada cewa an baiwa dukkan dalibai dama ba tare da la’akari da siyasa ba, madamar daliban ‘yan asalin Jihar Katsina ne kuma sun cancanta.

Wasu daga cikin masu gudanar aikin tantance daliban

An tantance daliban da suka nemi koyon aikin likitanci karkashin jagorancin kwamitin mutum 9 wanda mataimakin gwamnan jihar Katsina, Hon. Faruq Lawal Jobe da Shugaban Ma’aikata na Jiha, Alhaji Usman Isyaku suke jagoranta.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da kwamishinonin Ilimi mai zurfi da fasaha da koyar da sana’o’i da na kiwon lafiya, Akanta Janar na Jiha, shugaban  Hukumar Kula da Asibiti, shugaban Hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Katsina, Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi da Babban Sakatare na (Department of Establishment, Pension and Training).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here