Gina Jihar Katsina hakkin “yan Jihar Katsina ne

781

Daga Mohammad Lawal Maikudi

Gwamna Dikko Radda ya shiga sahun gaba na gwamnonin Nijeriya da suka himmatu wajen daukar mataksn biyan bukatun al’ummarsu a wannan karni.

Jihar Katsina tana cikin shiyyar Arewa Maso Yammacin Nijeriya wanda ya kunshi jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Jigawa, wato yankin da hada-hadar ta’addanci ta yi katutu duk da matakan da gwamnatin tarayya da gwamnaticin jihohin suka kwashe shekaru suna dauka ba tare da samun biyan bukata ba.
A lokuta da dama Gwamnatin Jihar Katsina ta sha gudanar da taron sulhu da ‘yan ya’adda domin samun maslaha, amma tarukan sulhun ba su cimma buri ba.
Wannan al’amari ya sanya Gwamna Radda ya yanke shawarar cewa ba zai yi zaman sulhu da ‘yan ta’adda ba. Ya ce ko dai su tuba, su ajiye makamansu, tare da neman afuwar jama’ar da suka zalunta ko kuma zai yi fito na fito da su, domin samar da zaman lafiya ko da dukiyar Jihar Katsina za ta kare akan hakan.
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina
To bisa dukkan alamu ‘ yan ta’addar ba su dauki shawarar mika wuya ba, hasali ma sai suka kara kaimi akan munanan ayyukansu. Shi kuma Gwamna Dikko Radda ya fara shirin tunkararsu.
Da farko ya yanke shawarar kafa rundunar tsaron al’umma inda aka zakulo zaratan matasa, aka ba su horaswa akan dabarun yakin sunkuru da bayar da bayanan sirri game da maboyar miyagu a sakuna da lungunan Jihar Katsina.
A ranar Talatar makon jiya Gwamna Dikko Radda ya yi bikin yaye wadannan zaratan matass a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke birnin Katsina.
A lokacin wancan biki an gabatar da motocin shiga daji, kirar Toyota Hillux kimanin 70 da babura kimanin 700 da sauran kayan aiki. Wannan mataki da Gwamna Radda ya dauka ya tabbatarwa jama’a cewa ya shirya murkushe ‘yan ta’adds da ta’addsnci a Jihar Katsina, ta yadda mutane za su ci gaba da rayuwarsu cikin natsuea da walwala.
Wannan harka ana gudanar da ita ta hannyar kashe makudan kudi.
Babban abin ttambaya a nan shi ne daga ina Gwamna Radda ya samo kudaden da ya ke wannan gagarimin aiki kuma ta ina zai ci gaba da samun kudaden da zai ci gaba amfani da su domin dorewar wannan muhimmin aiki, musamman ganin cewa kudin shigar da Gwamnatin Jihar Katsina ke samu ba su taka kara sun karya ba.
Alhaji Bello Kagara, Kwamishinan Kasafi da Tattalin Arziki na Jihar Katsina
Bayan wannan namijin kokari da Gwamna Dikko Radda ke yi domin samat fa zaman lafiya a Jihar Katsina, akwai batun bunkasa harkokin ilimi a Jihar Katsins. A halin da ake ciki Gwamnatin Dikko ta dauki malaman makaranta kimani 7000 domin koyarwa a makarantun firamare da na gaba firamare a cikin Jihar Katsina.
Wannan mataki zai taimaka wajen bunkasa! harkokin ilimi da rage yawan matasa majiya karfi da ke gararnnba a titi, wadanda kuma suna iya jawo matsalolin tsaro a cikin jama’a
Harkar daukar ma’aikata masu yawa babbar magana ce da ta ke bukatar kudade masu dimbin yawa. A nan ma akwai tambaya.
Daga ina Gwamna Dikko ya samo kudin gudanar da wannan aiki kuma daga ina zai ci gaba da samo su domin wannan gagarumin aikin gina Jihar Katsina ya dore?
A lokacin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta janye tallafin man fetur harkokin sufuri sun yi tsanani da tsada. Amma domin saukaka wa jama’a sai Gwamnatin Dikko Radda ta sayo motocin bas-bas guda 40, ta damka su ga hukumar sufuri ta Jihar Katsina tare da bayar da umurnin cewa kar ta kara adadin kudaden da ta ke karba a hannun fasinjoji.
A ranar Talatar makon jiya aka kaddamar da wadannan motoci a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke birnin Katsina. Shin daga ina Gwamna Dikko Radda ya samo kudaden da ya sayo wadannan motoci?
A farkon watan Okutoba Gwamnatin Dokta Dikko Radda ta bayyana cewa za ta tura dalibai 40 zuwa Kasar Misra domin su koyo karatun likita, wato ita za ta dauki nauyin karatunsu har su kammala bisa hasashen in sun dawo za su bayar da gudunmuwa a harkokin samar da lafiyat jama’ar Jihar Katsina.
Haka kuma bayanan da ke. kasa na nuna cewa Hukumar Bayar da Tallafin Karatu tana shirye shiryen biyan kudaden alawus na dalibai ‘yan asalin Jihar Katsina da ke manyan makarantun Nijeria. Shin ina Gwamna Dikko Radda ya samu kudaden yin wannan hidima?
Gwamnatin Dikko ta kaddamar da gina makarantun sakandare na mata guda 75 a wurare daban daban karkashin shirin AGILE a Jihar Katsina domin ‘yan Jihar Katsina. Shin ina Gwamna Radda ya samo kudaden wadannan ayyuka?
Wadannan ayyuka da muka bayyana a sama ana gudanar da su ne bayan na yau da kullum, musaaman irin abubuwan da suka shafi biyan albashi da alawus din ma’aikata a ko wane watan duniya.
Duk da wadannan aikace aikace da gwamnati ke gudanarwa domin inganta rayuwar. al’umma, akwai bayanan da ke nuna cewa kudin shigar da gwamnati ke samu a cikin gida bai kai naira biliyan daya ba.
Wannan babban kalubale ne ga kowane dan Jihar Katsina kuma wajibi ne a fito a gayawa juna gaskiys. Wato ya zama tilas jama’ar Jihar Katsina su tashi tsaye mazansu da matansu, manyansu da kananansu, domin fuskantar. wannan kalubale na bayar da gudunmuwa domin fuskantar wannan kalubale
Akwai akalla hanyoyi uku.
Hanya ta farko ita ce raka wannan gwamnati da addu’o’jn samun nasara bisa wadannan kyawawan ayyuka da ta sanya a gaba a duk inda dama ta. samu.
Na biyu shi ne bayar da goyon baya a wuraren da ta yi daidai, da shawarwari inda ake bukatar gyara ko gyare-gyare, sanya ido ga duk abubuwan da gwamnati ta yi don amfanin jama’a.
Na uku shi ne ko wane baligi ya saka hannu cikin aljihunsa domin bayar da gudunmuwar kudi domin ci gaba da wadannan kyawawan ayyuka. Wajibi ne kowane baligi dan Jihar Katsina ya bayar da wannan gudunmuwa gwargwadon samunsa.
Haka kuma kamfanoni da suke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina tilas a tiladta masu biyan haraji saboda ta wadannan hanyoyi ne za a samu kudaden samar da abubuwan ci gaba.
Alal misali, ko mutum bara ya ke yi, in babu zaman lafiya samun sadaka zai yi tsanani domin shi kansa mai niyyar bayar da sadakar yana cikin zullumi ta yadda neman halaliyarsa ke masa wuya.
Ya kamata manyan birane a Nijeriya irinsu Kano da Lagos da Kaduna sun bunkasa ne saboda kudin shigar da suke samu a cikin gida.
A lura cewa babu wasu mutane daga wasu wurare da za su kwaso kudinsu su kawo Jihar Katsina domin su bunkasa ta. Gina Jihar Katsina da bunkasa ta hakki ne na ‘yan Jihar Katsina
Saboda haka akwai bukatar Gwamnatin Jihar Katsina ta bullo da tsarin tara kudin shiga na cikin gida ta yadda duk wata naira da ta take hakkin gwamnati ta shiga asusun gwamnati kuma an yi amfani da ita wajen inganta rayuwar jama’ar Jihar Katsina.
Haka kuma wajibi ne gwamnati ta gano hanyoyin da kudin shigarta ke zurarewa kuma ta toshe su. Inda aka samu wani jami’i ko wasu jami’ai da laifin yi wa. gwamnati zagon kasa, to. wajibe ne a dauki matakin horo ko ladabtarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here