Gwamna Radda ya nada mataimaka na musamman kan harkokin siyasa

1070

Gwamna Radda yGwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya amince da nadin mataimaka na musamman kan harkokin siyasa na shiyyoyin dan majalisar dattawa da ake da su na Katsina, Daura da Funtua.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Arch. Ahmed Musa Dangiwa ta ce wadanda aka nada su ne Alhaji Habibu Sulaiman na shiyyar Funtua, Alhaji Halilu Ibrahim Karofi na shiyyar Katsina da Alhaji Hassan Kawuri na shiyyar Daura.

Bayanin hakan yana kunshe ne a wata takardar bayani da ta fito daga ofishin Babba. Sakataren Watssaa Labbsrai na Gwamnan Jihar Katsin, Mohammed Ibrahim Kaulss wadda ta ce Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya ce an nada su ne bisa cancanta da gamsuwar cewa za su yi aiki don jihar Katsina ta ci gaba.

Malam Dikko Umaru Radda PhD ya taya su murna bisa wannan dama da aka ba su ta su hidimta wa jihar Katsina. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi musu jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here