Ofishin yakin neman zaben shugaban Nijeriya na Jihar Katsina ya gudanar da walima tare da addu’oin samun nasarar sabuwar gwmanati ta Maigirma Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda da Zababben Sanatan Shiyar Katsina ta Tsakiya, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da dukkan wadanda suka samu nasarar a karkashin jam’iyyar APC.
Shugaban ofishin, Associate Professor Badamasi Lawal Charanchi ya fara bayyana cewa makasudin walinar shi ne yi wa wadanda suka samu nasarar lashe zaben da aka gudanar fatar alheri da addu’ar samun nasarar cika alkawuran da suka yi wa jama’a.
Babban sakataren ofishin, Alhaji Abubakar Bala Saulawa ya wakikci Farfesa Badamasi Lawal a wurin taron kuma ya yi fatan samun nasarar wadannan bayin Allah yayin gudanar da shugabancin su tare da wakilcin da al’umma suka dora masu don fidda su kunya musamman su da suka tallata su.
A yayin walimar an gabatar da addu’oi na neman albarka cikin gwamnatin tare da kira ga al’umma da kar su gajiya wajen yi masu addu’a don kawo sauyi mai alfano ga al’ummar kasar nan.
Walimar ta samu wakilan zababben Sanatan Shiyyar Katsina ta Tsakiya wanda Alhaji Umar Mati Saulawa ya wakilta tare da Alhaji Umar Farooq Ak, Alhaji Shehu Yusuf Saulawa, Alhaji Dahiru Abu Darma,
Walimar ta samu sanya albarka da tsohon kwamishinan lafiya na jihar katsina Alhaji Kabir Ibrahim Doro dadai sauran su.













