Gwamnatin Jihar Katsina ta sha alwashin bayar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomin jihar.
Gwamnan Jihar Katsina, Dokta Dokko Umar Radda ya bayyana haka yayin wani taro da shugabannin kananan hukumomin jihar a ofishinsa.
Bayanin haka ya fito ne daga ofishin Babban Mataimaki na Musamman akan kafafan sadarws na zamani ga Ga Gwamnan Jihar Katsina, Alh Isah Miqdad
Akan haka Dokta Radda ya umurci dukkan shugabannin kananan hukumomin da su ci gaba da zama a kananan hukumominsu, su rika kawo masa rahoto game da matsalolin tsaro a yankunansu
Akan haka Dokta Radda ya umurci dukkan shugabannin kananan hukumomin da su ci gaba da zama a kananan hukumominsu, su rika kawo masa rahoto a kullum game da matsalolin tsaro a yankunansu
Gwamna Radda ya bayyana cewa za a gudanar da kididdigar ma’aikatan gwamnatin jihar domin sanin adadin ma’aikatan za bayar da dama ga gwamnati ta san adadin albashinsu tare da tsara yadda za iya biyansu hakkokinsu.
Daga cikn wadanda suka halarci taron akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alh.Faruq Lawal Jobe; Sakataren Gwamnati, Arch. Ahmed Musa Dangiwa; Shugaban ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alh. Jabiru Salisu Tsauri; Babban Sakataren Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alh Abdullahi Aliyu Turaji; Akanta Janar Malik Anas da dukkan shugabannin kananan hukumomi.













