‘Yan sandan Adamawa sun cafke masu yukurin satar mutane

498

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wasu mutane biyar ‘yan asalin Kamaru bisa zargin yunkurin sace wani mutum mai suna Emmanuel Ebel, a Unguwar Jambutu da ke Yola fadarJihar Adamawa a Nijeriya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Suleiman Nguroje, ya bayyana haka cikin wata takardar sanarwar manema labarai ranar Asabar a Yola, yana mai cewa mummunan shirin da mutanen suka yi ya bayyana ne, biyo bayan samun bayanan sirrin da rundunar ta yi.

Ya ce samun bayanan sirrin ya bayar da damar samun nasarar dakile shirin da cafke mutanen da kuma wargaza mummunan shirin kafin su kai ga aiwatar da shi.

Yace “jami’an rundunar ‘yan sandan d aka kawo su jihar sun yi nasarar wargaza wani yunkurin garkuwa da Emmanuel Ebel, mazaunin Unguwar Jambutu a karamar hukumar Yola ta arewa.

“Rundunar ta samu bayanai sirri,  ta dauki matakan tsaro a yankin, da ya kai ga nasarar cafke mutanen da’ake zargin” in ii sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta bayyana sunsayen mutanen da ta kamen da Chubrandom Safinga, 30, Ibrahim Tala, 32, Ngosso Ndjombe, 28, Mmai Rostand, 32 da Nossu Ngambewo Ricky 27.

Yace “duk masu aikata miyagun ayyuka daga makwabciyarmu Kamaru za mu kame su mintuna 20 kafin su aiwatar da shirinsu.

“Kwamishinan ‘yan sanda CP Sikiru Akande, da jagororin OC SIB da jaruman Jami’an rundunar suna aiki ba ji ba gani domin tabbatar da ganin an kamesu, haka kuma ya umurcesu da su kara yi wa masu aikata miyagun ayyuka shiri da tsari” inji Nguroji.

SP Suleiman Nguroji, yabce Kwamishinan rundunar ‘yan sandan ya bukaci jama’a da su rika sanar da rundunar ayyukan miyagun mutane da inda suke zama.

Haka kuma ya baiwa gwamnati da jama’ar jihar tabbacin kokarin da rundunar ta ke yi na ganin ta kare rayuka da tsare dukiyoyin jama’ar jihar Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here