Gwamnatin Jihar Bauchi za ta shiga tsakanin Musulmi da Kirista

570

Daga Muazu Hardawa, Bauchi: Gwamnati Jihar Bauchi ta bayyana aniyarta na warware rikicin filin makabartar da wata gwamnati a baya ta ba jama’ar kirista da ke Bayara a karamar hukumar Bauchi, al’amarin da ya fara haifar da zaman tankiya tsakanin kirista da musulmi a yankin.

Al’ummar Yolan Bayara da ke bayan asibitin Bayara karkashin jagorancin Malam Sani Yakubu sun kira taron ‘yan Jarida ranar Lahadi inda suka bayyana korafin su kan an dauki filayen su na.gonaki masu murabbain hekta 50 an ba kiristocin yankin don su gina makabarta amma har yau babu wanda ya ba su diyyar ko Kobo, alhali sun gaji filayen ne daga iyaye da kakanni.

Akan haka sun bayyana cewa ba su yarda ba, suna bukatar gwamnati ta masu adalc,i a biya su diyya ko a bar su da filayen su in ana son zaman lafiya.

Kakakin gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Muktar Gidado da kwamishinan filaye da safiyo na Jihar Bauchi Alhaji Adamu Gabarin sun kira taron ‘yan jarida a ranar Lahadi a Gidan Gwamnati inda Muktar Gidado ya ce an ba su ( kiristoci) fili hekta 50 don gina makabarta a wata gwamnati da ta gabata har an ba su takardar shaida. Amma tun da wannan magana ta taso, wannan gwamnati a karkashin Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir za ta yi bincike daga hukumomin da suka dace don warware rigimar.

 Alhaji Muktar Gidado ya bayyana cewa filin da suka nema hekta 470 ne Kuma aka basu, Amma  yanzu korafi ya taso don haka aka kafa kwamitin bincike kan irin rigingimun filaye da ake fuskanta.

Kwamitin wanda ya ke karkashin shugabancin Mataimakin Gwamna Sanata Baba Tela tuni ya amshi  takardun korafi  na al’ummar kirista da musulmi kan cewa za a duba wannan bukata tasu a warware matsaloli da ake da korafi kansu a kowace kusurwa ta Jihar Bauchi.

Don haka ya ce kowane mutum a matsayin sa na dan kasa yana da damar neman ma’aikatar kasa da safiyo ta samar masa fili don gina makabarta, ko gida ko wani abu na ci gaba. Amma duk da cewa kasa ta gwamnati ce dole duk wanda ya mallaki fili idan aka karba don yin aikin ci gaba za a biya shi diyya.

 Don ganin akwai korafi daga wasu mutanen da suke tutiyar cewa filin su ne ba a biya su diyya ba ya bayyana cewa gwamnati tana kokarin ganin ta bi wannan magana don ganin masu korafi an bi malsu hakkokinsu, gwamnati ta yi abin da ya dace, ba tare da an cutar da kowa ba.

Ya ce nan ba da jimawa ba gwamnati za ta sanar da jawabin rahoton matsayar da ta dauka kan al’amarin yana mai cewa kowa ya kai zuciya nesa a ci gaba da zaman tare kanar  yadda ake yi kuma kowa za a bi masa hakkin sa ba cuta ba cutarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here