Muna tir da kisan ‘ya jarida. – Fasto Buru

850

An bayyana kisan ‘yan jarida da kuma musguna masu a matsayin abin bakin ciki da takaici musamman gani irin gagarumar gudunmuwar suke bayar ga ci gaban al’umma ko’ina cikin duniya a ko wane lokaci.

Bayanin haka ya fito daga bakin Fasto Yohana Buru, fitaccen malamin addinin Kirista, a wajen wata walimar da aka shiryawa manema labarai reshen Jihar Kaduna domin murnar shigowar shekarar 2023.

 Fasto Yohana Buru ya bayyana yan jarida a matsayin kashin bayan samun nasararsa a irin fafutikar da ya ke yi domin samar da zaman lafiya da kyakkyawan zamantakewa a tsakanin al’umma.

Fasto Buru ya ce ” hakika muna ganin irin yadda ‘yan jarida suke aiki a duniya da kuma abin da ake yi masu a duniya, saboda haka muke yin Allah wadai da abin da ake yi wa manema labarai, musamman yadda ake kashe su da kuma zuba su a cikin gidan kurkuku.;Don haka ba mu goyon baya. Muna bakin cikin hakan.

“Hakika ba domin irin yadda ‘yan jarida ke ta kokarin yada abubuwan da na ke yi a tsakanin al’umma na zaman lafiya da kwanciyar hankali da duniya ba ta san abin da na ke yi ba, amma sai ga shi a halin yanzu ina cikin sahun gaba da majalisar dinkin duniya ta san abin da na ke yi har aka bani lambar Yabo ta zaman lafiya. “

Shi kuma Madaucin Zazzau Hakimin Barnawa  Alhaji Kabiru Zubairu,kira ya yi ga al’umma da su kara yin kaimin yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban jama’a. “Muna kuma fatan samun shugabanni da za su jaddada adalci ga al’umma”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Sheikh Aliyu Turmutsi cewa ya yi su a matsayinsu na masu aikin samar da zaman lafiya suna farin jiki da abin da yan jarida suke yi.

“Muna fatan a samu mutane da yawa kamar irinsu Fasto Yohana Buru domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma”.

Bayanai sun nuna cewa tun da aka samu aiwatar da wani shiri karkashin jagorancin Fasto Buru, aka yi wasan kwallon kafa tsakanin matasan Tudun Wada Kaduna da kuma matasan Unguwar Gwanin Gora wanda hakan ya yi tasiri kwarai wajen samar da zaman lafiya da ci gaban jama’a.

Shugaban kungiyar masu sayar da shayi na Jihar Kaduna Malam Aliyu Yahaya godiya da jinjina ya yi ga yan jarida bisa irin kokarin da suke yi wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Mune muke aikin shayi a koda yaushe muke fita daga gidajen mu zuwa wuraren sayar da shayin mu tun da Asuba zuwa 12 koma karfe daya  na dare, wanda ba domin zaman lafiya ba da hakan bai samu ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here