Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman ya bayyana cewa indai Dikko Radda yana cikin takara to ba shi da zabin da ya wuce shi.
Ya faɗi haka ne a lokacin da dan takarar Gwamnan jihar Katsina na Jam’iyyar APC, Dokta Dikko Umar Radda ya kai ma shi ziyarar ban girma a fadar shi da ke Ƙofar Soro, Katsina ranar Lahadi, 1 ga Janairu 2023.
A lokacin ziyarar Dokta Dikko Raɗɗa ya bayyana ziyara a matsayin girmamawa da neman tabarraki na iyayen ƙasa sarakuna akan takarar sa ta neman gwamna da sauran ‘ yan takarkaru na Jam’iyyar APC a jihar Katsina.
Ya shaida wa sarki yadda tawagar sa suka zagaya kananan hukumomi sha tara (19) da mazabu sama da 170 na Jihar Katsina domin neman goyon bayan al’umma.
Ya shaida ea Mai Martana cewa yana da kundi wanda zai shugabanci al’umma idan Allah ya ba shi nasara wanda ya haɗa da hanyoyin magance matsalar tsaro, farfaɗo da harkar ilimi, lafiya da hanyoyin samar da aiki ga matasa, mata, da masu kananan ƙarfi.
A fannin ilimi ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta assasa makarantu na gwamnati na musamman, aƙalla guda daya a kowace shiyya, domin ɗaukar yara masu basira. Sa’annan za su inganta harkokin lafiya ta hanyar ɗaukar likitoci wadanda za a ba su horo na musamman domin su zauna a kananan hukumomin su saboda karancin likitoci da jihar ke fuskanta.
A kokacin da ya ke jawabi, Mai Martaba sarki ya yi farin ciki akan wannan ziyara inda ya bayyana ta a matsayin zumunci domin dan takarar gida yazo.
Ya ce Dokta Dikko Raɗɗa mutum ne mai nagarta da sanin girman nagaba kuma dan uwa na jini. A sabili da haka yana tare da shi akan aniyar sa ta zama Gwamnan Jihar Katsina.
Mai Martaba Sarkin Katsina ya yi kira a gare shi da ya ji tsoron Allah ya kare hakkin talaka idan Allah ya ba shi nasara, domin Allah zai tambaye shi a gobe ƙiyama yadda ya gudanar da shugabanci. Daga karshe ya yi addu’a samun nasara da fatan alkhairi.