Dokta Dikko ya binne PDP a Danmusa

539

Ɗan takarar Gwamnan  Jihar Katsina na Jam’iyyar APC, Dokta Dikko Umar Raɗɗa ya jijjiga Karamar Hukumar Ɗanmusa inda dubban magoya baya suka yi dafifi domin tarbar shi a ci gaba da yaƙin neman zaɓensa da ya guda a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba 2022.

Tawagar wadda ta ƙunshi jigajigan Jam’iyyar APC sun isa fadar Hakimin Danmusa bayan gaisuwa da suka fara kai ma Sarkin Fulanin Dangi, Hakimin Yantumaki, domin neman tubarraki da goyon baya daga masarautu, limamai da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar.

Tawagar ta shafe aƙalla sama da awa ɗaya da rabi daga fadar Hakimin Ɗanmusa zuwa sakatariya ta karamar hukuma, inda Dr. Raɗɗa ya ƙaddamar da motoci guda biyu da babura talatin (30) ga Sojoji da Shugabannin Jam’iyya wanda Shugaban Karamar hukumar Ɗanmusa, Hon. Sanusi Abbas Dangi ya bada.

A lokacin da tawagar ta isa filin taron, babu masaka tsinke domin kuwa dubban masoya, maza da mata ne suka yi cincirindo wajen gane ma idon su tsarabar da ɗan takarar ya zo masu da ita.

A lokacin da yake jawabi, Dokta Dikko Raɗɗa ya fara da nuna farin cikin shi a fili don ganin yadda al’ummar Ɗanmusa suka amsa kiran Jam’iyyar APC. Ya bayyana karamar hukumar a matsayin wadda Allah ya albarkace ta da wasu muhimman mutane wanda aka amfana da su da cigaban da suka kawo, sabanin wasu mutane da suka samu dama ba su taimaki al’umma ba.

Ya ci gaba da cewa ya san babban abun da ya dami al’ummar Ɗanmusa wanda shine matsalar tsaro. A sabili da haka ya ba su tabbacin cewa yana da kyakyawan tsari da ya yi na sha’anin tsaro wanda cikin amincewar Allah zai zamo silar kawo karshen matsalar a Jihar Katsina.

Haka kuma ya sha alwashin ba matasa da mata jari na yin sana’oi domin bunkasa tattalin arzikinsu da na Jihar Katsina da kuma samar da aikin yi ga al’ummar Katsina baki daya.

Taron ya samu halartar  dan takarar mataimakin gwamna, Hon. Faruq Jobe, Shugaban Kwamitin yakin neman zaben APC na jihar Katsina, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Hon. Bala Abu Musawa, Hon. Garba Sai baba, Hon. Sanusi Abbas Dangi, Col. Abdulaziz Musa Yar’adua, Hon. Abdulkadir Zakka, Hon. Musa Adamu Funtua, Hon. Jabiru Tsauri, Hon. Abdullahi Aliyu Musawa, Hon. Abubakar Sukaiman Korau, Hon. Usman Banye, Injiniya Surajo Yazid Abukur da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here