A ci gaba da gangamin yakin neman zabe, a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022, tawagar dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin jamiyar APC, Dokta Dikko Umaru Raɗɗa ta sauka a Karamar Hukumar Batsari.
A lokacin da tawagar ta isa Batsari Dokta Raɗɗa ya jagorance ta zuwa kai gaisuwar ban girma da neman tabarakin iyayen ƙasa a Fadar Gado Da Masun Katsina, Hakimin Wagini, Alh. Dikko Mu’azu Ruma da ke garin Wagini inda ya gana da hakimin da sauran dagattai na gundumar kafin zarcewa zuwa fadar Sarkin Ruma, Hakimin Batsari da ke a garin Batsari inda anan ma ya gana da hakimi da magaddai.
Bayan gaisuwar ban girma da neman tabarrakin shugabanin alumna, tawwagar ta wuce zuwa filin da aka shirya ganawa da al’umna a filin taro.
Da ya ke jawabi ga dimbin jama’ar da suka tarbe shi, Dokta. Raɗɗa ya jajantawa al’ummar Batsari kan matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin tsawon shekaru tare da bayar da tabbacin yin kokarin sa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar idan aka zabe shi.
Ya shaida cewa, ko da kuɗin jihar za su ƙare a kan kawo karshen matsalar tsaro, to zai yi amfani da su domin kawo zaman lafiya a jihar Katsina. Ya kuma ba su tabbacin kawo kyakywan shugabanci wanda jihar za ta yi alfahari da shi.
Dokta Radda ya kuma yi amfani da damar wajen sanar da al’ummar yankin yadda ya kuduri aniyar kawo sauyi a harkar noma da kuma bullo da kananan masana’antu da sarrafa kayan gona a fadin jihar.
Yayin da ya ke kira ga al’ummar yankin da su zaɓi daukacin ‘yan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, Dokta Dikko ya gode musu bisa kyakkyawar tarba da suka yi masa da mukarrabansa.
Sauran wadanda suka yi jawabi a lokacin yakin neman zaben sun hada da shugaban jam’iyyar APC na jiha, Alh. Sani Aliyu Daura, Shugaban kwamitin yakin neman zabe Dikko/Jobs, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Shugaban Karamar Hukamar Batsari, Hon. Yusuf Mamman Ifo, Dan takarar Sanata na Katsina ta tsakiya, Col. Abdulaziz Musa Yar’adua da sauran ‘yan takarar APC na shiyyar.