Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya bayyana gamsuwar sa a bisa yadda mutanen Jibia suka yi cincirindo wajen nuna ma Jamiyyar APC goyon baya wanda ya ce ba komai ba ne illa nuna godiya ga yadda gwamnatin APC ta kawo ci gaba a yankin su. Ya shaida cewa a shekarar 2019 sun yi taro a Jibia kuma sun samu kuri’u a zaben, don haka suna fata za a linka abun da ya fi haka.
Tun farko twagar dan takarar gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dokta Dikko Umar Radda ta samu kyakkyawar tarya a Karamar Hukumar Jibiya a ci gaba da yakin neman zabe a shiyyar Katsina ta Tsakiya a ranar Talata.
Garin Jibiya ya cika ya batse da dimbin masoya da magoyan APC da Dokta Dikko Umar Radda da sauran masu takarar mukamai daban daban a karkashin jam’ iyyar APC.
Tawagar ta fara yada zango ne a mazaɓar Rico inda ta samu tarba ta karamchi da nuna ƙauna daga al’ummar mazaɓar. Dokta Dikko ya yi masu alkawarin hanya da za ta taso daga ‘Yar kutungu zuwa Rico domin inganta rayuwar su idan Allah ya ba shi nasara.
Daga bisani tawagar ta nufi fadar Mai Girma Ɗan Madamin Katsina, Hakimin Ɗaɗɗara, Alh. Usman Usman Nagogo, domin neman tabarraki da goyon baya. Danmadamin Katsinan ya bayar da tabbacin goyon bayan sa da na mutanen ƙasar shi akan tafiyar Dr Dikko Radda da APC.
Tawagar neman zaben ta ziyarci sauran mazaɓu kamar Bugaje, Kusa, Mazanya, Gangara, kafin ta isa fadar Mai Girma Sarkin Arewa, Hakimin Jibia, domin neman albarka da kuma goyon baya.
A lokacin da ake gudanar da gangamin yakin neman zaɓen, dubunnan al’umma ne magoya baya suka yi cincirindo da dafifi wajen gudanar da taron, wanda tawagar ta share sama da sa’i biyu kafin shiga filin saboda yadda al’umma suka fito kwan su da kwalkwata domin nuna goyon baya.
Shugaban Karamar Hukumar Jibia, Hon. Sabiu Maitan, a lokacin da ya ke jawabi, ya bayyana cewa babu sauran wata jam’iyya a Jibia banda APC, domin kuwa a rana mai kamar ta yau, sun nuna ma al’ummar Katsina cewa Karamar Hukumar Jibia ta APC ce, kuma za su sa a zaɓe ta a zaɓe mai zuwa saboda ayyukan alkhairi da Jamiyyar ta yi masu.
A lokacin da ya ke jawabi, Dokta Dikko Raɗɗa, ya bayyana farin ciki da jin daɗin shi marar misaltuwa ga yadda al’ummar Jibia suka nuna mashi ƙauna da soyayya, wanda ya shaida masu cewa ko da kuɗin jihar Katsina za su ƙare wajen magance matsalar tsaro, to zai yi amfani da su don ganin al’umma sun yi bacci da ido biyu.
Ya ci gaba da cewa, za ya farfaɗo da harkokin noma domin bunƙasa tattalin ariziƙi da kuma haɓɓaka harkar ilimi domin samun ilimi ingantacce idan Allah ya ba shi nasarar lashe zaben 2023.
Daga karshe ya roƙi alfarmar su da goyon bayan su akan zabar Jam’iyyar APC a dukkan matakai a lokacin zabe.
Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Ɗan Takarar Gwamnan da mataimakin sa, Dr. Dikko Radda da Faruq Lawal Jobe, Shugaban Jamiyyar APC na Katsina, Hon. Sani Aliyu JB, Mataimakin Shugaban Jamiyya, Alh. Bala Abu Musawa, Darakta na yakin neman zabe, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Dan Takarar Sanata na Katsina ta tsakiya, Col. Abdulaziz Musa Yar’adua, Ɗan Takarar Majalisar wakilai mai wakiltar Kaita/Jibia, Hon. Sada Soli Jibia, Mataimakan Darkata na yakin neman zabe, Hon. Musa Adamu Funtua, Prof. Badamasi Charanchi, Hon. Jabiru Tsauri, Yan majalisun Dokoki na jihar Katsina, Kwamishinoni, Shugabannin kananan hukumomi da sauran magoya baya.