KATSINA 2023: Jirgin neman zaben Dikko Radda ya sauka a Kaita

727

Bayan kammala yaƙin neman zaɓensa a kananan hukumomi 12 da Mazaɓu 128 daga shiyyar Daura, Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta dawo yaƙin neman zaɓenta na gwamna da sauran yan takarkaru a jihar Katsina bayan hutun kwanaki 7.

Idan dai za a iya tunawa, an ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna a Karamar Hukumar Faskari da ke jihar a farkon watan Disamba tare da dimbin magoya bayansa.

An ci gaba da yaƙin neman zaɓen ne a ranar Litinin, 26 ga watan Disamba 2022, a shiyyar Katsina ta tsakiya a karamar hukumar Kaita.

 Ziyarar da aka yi a shiyyar Daura ya samar da goyon bayan da ba a taba ganin irinsa ba ga dan takarar da jam’iyyar APC. Tawagar yaƙin neman zaɓen Dikko/Joɓe ne suka karfafa kamfen din shiyyar Katsina ta tsakiya zai kuma kara karfafa nasarorin da aka samu a Daura.

Dokta Dikko Raɗɗa a lokacin yaƙin neman zaɓen yace, “ziyartar al’umma da suke yi a matakin mazabu shi ne don yi ma su fatan samun ingantacciyar rayuwa a ƙarƙashin gwamnati mai zuwa a matakin jiha da tarayya. Hakan zai baiwa gwamna mai jiran gado damar samun haƙiƙanin halin da al’ummar jihar ke ciki.

Dokta Raɗɗa ya buƙaci al’ummar yankin da su fito fili su ba da

goyon bayansu ga tikitin Dikko/Jobe a zaɓen 2023 domin kara tabbatar da nasarorin da gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta samu.

Taron ya samu halartar Dan Takarar Gwamnan da mataimakin sa, Dr. Dikko Raɗda da Hon. Faruq Lawal Joɓe, Shugaban Jamiyyar APC, Hon. Sani Aliyu Daura, Shugaban kwamitin yakin neman zaɓe, Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, Tsohon gwamnan Borno, Col. Abdulmumin Aminu, Ɗan Takarar Majalisar Dattijai na Katsina ta Tsakiya, Kanar. Abdulaziz Musa Yar’adua, Hon. Sada Soli Jibia, Yan Majalisun jiha, Yan majalisar zartaswa na jihar Katsina, Shugabannin kananan hukumomi, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here