Daga Imrana Abdullahi: Shugaba Muhammadu Buhari, ya nada Injiniya Tukur Muhammad Lawal Funtuwa, a matsayin Manajan Daraktan hukumar kula da tauraron dan Adam (NIGCOMSAT).
Kamar yadda wata takardar mai dauke da sa hannun Uwa Suleiman, babbar mai taimakawa ta musamman da kuma magana da yawun ministan ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki da ake samu ta hanyar amfani da yanar Gizo, ta bayyana ta ce Tukur Funtuwa ya gaji tsohon Manajan Daraktan hukumar ne da ya ajiye aiki Dokta Abimbola Alale.
An haifi Injiniya Tukur Mohammed Lawal Funtuwa, ne a ranar 24 ga watan Nuwamba 1966 kuma shi dan asalin karamar hukumar Funtuwa ne da ke cikin Jihar Katsina a Arewa ta Yamma a Tarayyar Najeriya.
Ya yi karatun sa na digiri a Kemikal injiniya, ya samu babbar Difiloma ta PGDM, da kuma digiri na biyu sai kuma Difiloma a fannin kwarewa a bangaren ilimi da kuma digiri na uku a kan fannin kula da ci gaban jagoranci wanda yake jira a halin yanzu ( in view) saga jami’ar Fatakwal.
Kafin nadimsa ya kasance Darakta ne a kamfanin siminti na BUA ya kuma yi aiki a bangarori da dama da suka hada da kula da lafiya, manajan shiyya mai kula da sadarwa da al’amuran jama’a a kamfanin Lafarge na Afrika da kuma aiki a kamfanin siminti na Dangote mai kula da harkar muhalli da abubuwan da suka shafi jama’a duk a kamfanin Siminti na Dangote da dai wadansu bangarori da dama.
Idan dai za a iya tunawa wannan hukuma da ke kula da na’urar Tauraron dan Adam (NIGCOMSAT) tana a karkashin ma’aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arzikin da ake samu ta hanyar amfani da yanar Gizo.