KATSINA: Sakon PDP ga APC

875

Daga Mohammad Lawal Maikudi: A ranar Talata jam’iyyar PDP ta gudanar da taron gangamin neman shugaban kasa a birnin Katsina, hedikwatar Jihar Katsina domin tallata dan takararta, Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa.

Taron ya samu halarcin manyan shugabanni da magoya bayan PDP daga sassa daban daban na Nijeria. Masu nazari da sharhi akan harkokin siyasa, musamman dangane da shirye shiyen zabukan 2023 na nuna cewa wannan taron gangamin ya fi jan hankali fiye da sauran da suka gabace.
Ganin irin jiga jigan jam’iyyar da suka halarci taron da kuma adadin mutanen da suka cika filin wasan tunawa da Muhammadu Dikko akwai manyan batutuwa biyu zuwa uku da suka bayyana a fili.
Da farko PDP ta nuna cewa tana nan da rai, akasin yadda wadansu suke tunanin cewa ta mutu murus, musamman a Jihar Katsina inda ko mukamin kansila ba ta da shi a tsawon kimanin shekaru takwas.
Jihar Katsina na cikin jihohin da APC ta wanke tun 2015 kuma har ya zuwa yanzu an hana  PDP rawar gaban hantsi, duk da cewa ta kwashe shekaru 16 ta mulkin jihar kafin zuwan APC.
Watakila PDP ta gudanar da wancan gangami domin ta nunawa APC galabar da ta samu a 2015 da 2019 ba za ta samu 2023 ba. Wani abin tunawa shi ne Jihar Katsina ta samar da kuri’u kimanin miliyan daya a zaben shugaban kasa. Yanzu ta shirya canza wancan al’amari.
Haka kuma akwai masu ganin an daura damarar yaki ne da Shugaba Buhari, aka iske shi har gida domin a tozarta shi, a nuna cewa soyayyar da ke tsakanin shi da jama’ar jiharsa ta dushe kuma sun dawo daga rakiyarsa da abin da ya ke talla, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Babu shakka karsashin son Shugaba Shugaba Buhari ya raunana sakamakon matsolin tsaro da na rayuwar yau da kullum, amma dai akwai masu tunanin cewa har yanzu akwai kyakkywan zato tsakanin ‘yan Nijeriya da Shugaba Buhari, kuma muddin ya yi kira za su amsa.
Wani abin lura ga taron PDP na ranar Talata shi ne sako ga jam’iyyar APC mai mulki da wadanda suke jagorancita da kuma gwamnatin jiha cewa kar su saki jiki cewa sun kashe PDP sun kuma rufe ta. In dai suna son su tsira da mutuncinsu da na jam’iyyarsu, sai sun mike tsaye sun yi jan aiki.
Amma babu shakka Jihar Katsina na cikin jihohin da za a yi gumurzu tsakanin APC da PDP a zaben shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here