An cinna wuta a ofishin PDP na Gombe

605

A yau da safe wasu mutane da ba a tantance su ba suka cinna wuta a ofishin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na Jihar Gombe da ke Arewa Maso Gabashin Nigeriya.

Ofishin dai ya kunshi  yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Gombe Mohammed Jibrin Barde.

da dankarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar kuma yana daf da

fadar Gwamnatin Jihar Gombe.

Sai dai PDP ta zargi Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da hannu, tana mai cewa “’Yan daba sun kai hari Oifhin Yakin Neman Zaben Barde da sanyin safiyar yau Litinin, kuma muna zargin APC na da hannu a ciki.

“Wannan harin daya ne bayan wasu da dama da aka kai mana a ’yan watatnnin nan, wanda ke nuna gwamnatin nan ta dauki salon tashin hankali, kuma dole ne a yi tir da shi,” in ji Junaidu Usman Abubakar.Mataimakin Kakakin Yakin Neman Zaben Atiku/Barde a Jihar Gombe.

i

Alhaji Ismaila Uba Misilli, Darakta-Janar na Yada Labaran Gwamna Inuwa Yahaya, kan lamarin, amma ya ce zai waiwaye shi daga baya.

Amma Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da harin, tare da cewa sun fara bincike da nufin cafko maharan.

Aminiya ta gano duk da yarjeneniyar zaman lafiya da ’yan siyasar jihar suka sanya hannu a kai gabanin zaben 2023, an samu karuwar rikicin siyasa a jihar.

Shi kansa ofishin na PDP da aka kona, a watan Agusta an kai masa hari tare da farfasa shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here