Tinubu ya amince da Sa’adu Gulma a Shugaban ‘Yan Arewa na APC a Legas

798

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas,  ya amince da Sa’adu Yusuf Gulma a matsayin Shugaban Al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas na Jam’iyyar APC, lamarin da ya warware matsalar shugabanci da ta kunno kai kuma ta dabaibaye al’ummar Arewa mazauna Birnin Ikko, wato Legas.

Asiwaju Bola Tinubu ya kawo ƙarshen rikicin ne a ranar Juma’a, 18 ga Nuwamba, 2022, bayan da ya amince da rahoton kwamitin da ya kafa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Alhaji Lawal Abbas Garba a matsayin Sakataren Kwamitin.

Haka kuma Asiwaju Bola Tinubu ya amince da Alhaji Aminu Dogara Yaro a matsayin Sarkin Hausawan Jihar Legas, yayin da Dr. Mohammad Banbado zai ci gaba da kasancewa Sarkin Fulanin Legas.

Idan za a iya tunawa, Tinubu ya naɗa kwamitin haɗaka ne bisa damuwarsa da yadda rikicin shugabanci ya kunno kai tsakanin al’ummomin Arewa mazauna Jihar Legas, inda a jiya ya amince da rahoton kwamitin bayan ya karɓe shi daga hannun shugabannin kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here