Za mu bunkasar hardar Alkura’ani a Jihar Katsina -Dokta Dikko Radda

768

Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana cewa a cikin kudirorin da ya ke kokarin kawowa domin neman gyaran al’amurra a Jihar Katsina zai kawo tsarin makarantun hardar Alkur’ani mai tsarki a Jihar Katsina.

Dokta Dikko Umar Radda wanda dan takarar Gwamna Jihar Katsina ya bayyana haka ne a wajen wani babban taron da  ‘yan asalin Jihar Katsina mazauna Kaduna da aka yi a garin Kaduna.

Dokta Radda ya ce za a yi ingantaccen tsari ne na makarantu masu inganci guda Uku kowace shiyya a yi makaranta guda daya, da za a inganta ta, a samar mata  kwararrun malamai, litattafai da kuma kayan koyo da koyarwa irin na zamani.

 Za a rika koyar da ilimin Lissafi da turanci da yadda komai zai samu inganta a samu mahaddatan Kur’ani kuma masana ilimin zamani ta yadda al’umma za ta inganta sosai.

Haka kuma za a samar da tsarin da wadannan mahaddata Kur’ani za su ci gaba da karatun jami’a har sai sun yi digiri kamar yadda ake yi a duk duniya.

“Ta yaya za a ce wanda ya yi karatun Alkur’ani har ya haddace shi amma kuma a rika daukar shi kamar bai yi ilimi ba? Ni a wuri na mutum ne wanda babu mai iliminsa a ko’ina za a laluba cikin duniya domin Kur’ani ya hada dukkan komai domin duk wani ilimi a nan za a same shi.

 Saboda haka ina gaya maku cewa mahaddata Kur’ani na da kima da darajar da babu mai ita ko a wurin Allah madaukakin Sarki don haka suna da gurbi mai yawa a cikin Gwamnatin Jihar Katsina”.

Dokta Dikko Umar Radda ya kuma yi bayanin cewa “Zamu dauki alkalummansu mu ga yawansu da abin da za a yi masu da nufin rayuwarsu ta inganta”, inji shi.

Kuma a kauyuka za a yi wani tsarin koya wa makarantar Allo da na Alkur’ani, ilimin lissafi da Turanci domin a samu daidaitawa da zamani, ta yadda za su iya ci gaba da karatunsu a duk jami’ar da suke bukata.

Dokta Dikko Radda ya ce za a samar da wani ingantaccen tsarin taimakawa matasa domin bunkasa rayuwarsu ta fuskar kula da harkokin wasanni kasancewar wannan bangare ya zama wata siyasar da take hada kowa da kowa a wuri daya ta fuskar hadin kai a duniya.

Kuma tsari ne da ya zama ana samun abin duniya da shi da har akwai wanda ya yi wasan kwallon kafa a duniya kuma ya zama shugaban kasar Laberiya, akwai kuma wadanda ke amfanar rayuwar jama’a da dama ta hanyar gudanar da rayuwar duniya a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here