PDP ta bunkasa da muatane 5,000 a Kano

853

Babbar jam”iyyar adawa adawa aKani da tarayyar Nijeriya, PDP ta bunkasa da magoya baya 5,000 a Karamar Hukumar Dawakin Today ta Jihar Kano.

Bayanin haka ya bayyana be a lokacin da Dan takarar Gwamnan Kano Jam’iyyar PDP Alhaji Sadq Aminu Wali ya ziyarci Dawanau domin Bude ofishin taking mean zabeda Kuma yin maraba da waddanda suka shiga PDP daga jam’iyyub APC da NNPP.

Rahotanni na nuna cewa waddanda suka canza Shekar sun had da matasa Maza da mata, waddanda su ne kashin bayan harkokin siyasa da zabe.

A lokacin ikin karbar sabbin magoya baya jam’iyyar a harabar Ofishin Jamiyyar PDP, na Dawakin Tofa, Hon Sadiq Wali, ya yi kira a garesu da su tabbatar da nasarar Jamiyyar PDP a kowanne mataki sakamakon gazawar da Jamiyya APC ta yi tareda  jefa al’umma cikin mayuwacin hali, na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Ya ce ya zama wajibi ga al’ummar wannan kasa su zabi Jam’iyyar PDP,  domin Ita kadai ce za ta farfado da wannan kasa daga cikin mayuwacin hali da take ciki.

Tawagar Dan Takarar Gwawmnan ta kunshi Hon. Yusif  Bello Danbatta, Dan Takarar mataimakin Gwawmna da Hon Saidu Gwadabe Gwarzo, Dan Takarar Sanata na Kano ta Arewa a Jamiyyar PDP, da Shugabanin Riko na Jamiyyar PDP a Jihar Kano, da sauran masu ruwa da tsaki na Jamiyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here