KATSINA: PDP ta dakatar da Sanata Yakubu Lado

1601

Rahitanni daga Katsina na nuna cewar jam’iyyar PDP tadakatar da Sanata Yakubu Lado Danmarke daga jam’iyyar

Sanata Yakubu Lado Danmarke shi be ke yi wa PDP takarar Gwamnan Jihar Katsina a zaben 2023.

Bayanin dakatarwar ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin gudanarwa na jam iyyar PDP karkashin jagorancin Alhaji Salisu lawal Uli.

Katsina City News ta ambato

Alhaji Salisu Lawal Uli yana cewa cikin yan kwamitin gudanarwar su 14, muatane 11 tare da ciyamomin kananan hukumomi 26 na jam iyyar suka amincewa da dakatarwar Sanata YAKUBU LADO.

Alhaji salisu Uli yace,sun dakatar da SANATA YAKUBU Lado ne bisa zargin yi wa jam iyya zagon kasa da makirci da bata mata suna.

Alh. Salisu Uli,ya ce sun dogara da sashen kudin tsarin mulki na jam’iyyar PDP sashe na 57  cikin baka 3.da sashe na 58, yana Mai cewa Jam iyyar PDP a Jihar katsina tana kara jaddada goyon bayan ta da sallamawarta ga shugabancin jam iyyar na kasa, karkashin dakta Iyochia Ayu.

Alh. Salisu Uli ya ce  tuni har sun aika da takardar dakatarwar ga uwar jam iyyar PDP ta kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here